kungiyar Buhari/Osinbajo (BOCO) ta shirya tsaf domin gudanar da gangami na musamman domin wayar da kan al’umma a kan muhimmancin zama lafiya a kasa baki daya.
Shugaban kungiyar ta kasa, Alhaj Isa Aminu Bayero ne ya sanar da hakan a lokacin da yake zantawa da wakilin Aminiya, inda ya ce wannan kungiyar it ace kungiyar da a da ake kira kungiyar fafutukar neman zaben Buhari (BCO), inda ya ce sun canza sunan kungiyar domin su hada da sunan Osinbajo.
“Mun shirya tsaf domin mu fadada ayyukanmu, wannan ne yasa muka hada da mataimakin shugaban kaska farfesa Yemi Osinbajo. Domin haka ne muka kuma kungiyar fafutukar neman zaben Buhari/Osibanjo (BOCO),” inji shi.
Bayero ya ce sun shirya gudanar da gangamin ne domin fadakar da mutane muhimmancin zama lafiya, musamman a daidai lokacin da kasar ke fusakantar barazana daga kungiyar IPOB masu fafutukar ballewa daga kasar.
Alhaji Isa ya kara da cewa, fafutukar da kungiyar ta IPOB ke yi bas hi bane abu mafi muhimmanci a wannan lokaci, inda y ace kasar nan ta kowa ce, don haka babu wani mutum ko wata kungiya da ta isa ta kori wani daga bangaren da suke.
Sannan a karshe ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari bisa yadda ya fuskanci matsalar ta masu neman ballewa, cin hanci da rashawa, rikicin kabilanci da kuma rikicin manoma da makiyaya.