Kungiyar Alarammomi ta Jihar Kano, Hisburrahman Fi tilawatil Kur’an ta yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta waiwaye su don cika alkawarin da ta daukar musu, na gina musu wurin karatun Alkur’ani a Unguwar Rijiyar Lemo da ke yankin Karamar Hukumar Dala, a Jihar Kano .
Shugaban Kungiyar Alaramma Tukur Ladan ne ya bayyana haka, a lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Kano.
Alaramma Tukur Ladan ya bayyana cewa kimanin shekara guda gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ta je ta ga mazaunin makrantar tare da yin alkawarin gina musu inda har ta umarce su su biya kudin na gani ina so na Naira dubu 40 daga wurinsu.
“A lokacin da muka gabatar wa gwamnati bukatarmu cewa muna so ta gina mana wurin karatun Alkur’ani, sai ta amince, inda har ta turo jami’anta daga ma’aikatar kasa da safiyo suka zo suka duba wurin tare da umartar mu akan mu hada Naira dubu 40 inda muka je Bankin Jaiz muka biya. An nuna mana cewa za a gina mana makarantar kan kudi Naira miliyan 40. Don Allah gwamnati ta taimaka mana kamar yadda take taimakawa sauran jam’ar jihar”.
Alaraman ya kuma bayyana takaicinsa, game da yadda shugabanni a kowane mataki suke nuna wa harkar almajirranci halin ko-oho, inda ya yi kira gare su da su waiwayi al’umma, musamman ma ganin cewa talakawa na cikin wani hai na ni ‘yasu.
“Talakawa na cikin halin yunwa da fatara, ga zaman zullumi na rashin tsaro da ake ciki a kasar nan. Don haka muke kira ga shugabanni da su taimaka mana”. In ji Alaramma Tukur Ladan