✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kungiya ta raba kayan sanyi ga kananan yara a Jama’a

Babban mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna kan harkokin shari’a, Barista Rabi Adamu Musa, tare da hadin gwiwar kungiyar Hafsatscrowd ta rabawa kananan yara kimanin 100…

Babban mai taimakawa gwamnan jihar Kaduna kan harkokin shari’a, Barista Rabi Adamu Musa, tare da hadin gwiwar kungiyar Hafsatscrowd ta rabawa kananan yara kimanin 100 kayayyakin sanyi da suka hada da suwaita da safa a yankin karamar hukumar Jama’a da ke jihar Kaduna.

Yayin da take jawabi bayan kammala rabon kayayyakin da aka gudanar a Kafanchan, Barista Rabi Adamu, ta ce lura da irin halin sanyin da ake ciki zai yi matuqar kyau a tuna da kananan yara marasa galihu don tallafa musu da kayayyakin sanyi.

“Wannan shi ne dalilin mu na na zabo yara 100 daga gundumomi hudu na Jama’a ta Tsakiya da ke Karamar hukumar Jama’a don tallafa musu da kayayyakin.” In ji ta.

Daya daga cikin wadanda suka amfana da rigunan sanyi da safa, Hosea John, ya bayyana farin cikinsa da tunawa da su a lokacin da ake bukatar taimakon saboda dawowar sanyi a yankin.