kungiyar Hausa ta Jami’ar Al-kalam da ke Katsina ta karrama wakilin Aminiya na Jihar Katsina, Malam Ahmad Kabir S/Kuka. kungiyar ta karrama shi ne da lambar yabo ta Kakakin Al’adun Hausa a bikin makon Hausa na jami’ar na bana.
kungiyar ta ce wakilin Aminiyar yana kokari yada muradun kungiyar na yada al’adun Hausa ta hanyar rubuce-rubuce da shirye-shirye, don haka ta ga ya dace ta karrama shi. Haka kuma ta ce wakilin na Aminiya ya bude wani zaure mai suna Asalin Hausa da Bahaushe a kafofin sadarwa na zamani irin su Whattsapp da Facebook wanda ya tattara mutane daga ciki da wajen Najeriya.
Sauran wadanda aka karrama, akwai ’yan jarida Rabi’atu Kabir Runka da Ibrahim Abdullahi Dutsinma da mawaki Aminu Alan Waka da Injiniya Muttaka Rabe Darma da Babban Jojin Jihar Katsina Mai shari’a Musa danladi da Uwargidan Gwamnan Jihar Katsina wadda aka ba Gimbiyar Hausa, kamar yadda taron ya wakana a dakin taro na Jami’ar Alkalam da ke Katsina a ranar 22 ga watan Satumban nan.