Gwamnan Jihar jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, ya ce a kullum da talaka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake kwana ya tashi a ransa.
Gwamnan, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin zabukan fid da gwani na Gwamnonin APC ya bayyana hakan ne a cikin shirin siyasa na Politics Today nan na gidan talabijin na Channels.
- NAJERIYA A YAU: APC A Idon ’Yan Najeriya Bayan Ta Tara Fiye Da N20bn
- Tsohuwar matar shugaban APC ta fito takarar Gwamnan Nasarawa
Badaru ya ce, “Shugaban Kasa yana gudanar da ayyukan gwamnatinsa tsakani da Allah. Kuma a kodayaushe yakan kwana ya kuma tashi da talaka a ransa; tare da tunanin ta ya ya zai inganta rayuwar shi.
“A lokacin da muka karbi kasar nan daga hannaun PDP, abubuwa sun riga da sun tabarbare, duk da cewa ana sayar da gangar danyen mai akan Dala 80, amma a wancan lokacin akwai Jihohi akalla 26 da ko albashi ba sa iya biya, duba da irin aika-aikar da PDP ta yi a lokacinta, saboda haka, ina da yakinin cewa ’yan Najeriya ba za su sake zaben ta ba,” inji shi.
Badaru ya kuma ce yana da yakinin cewa ko a babban zabe mai zuwa na shekara ta 2023, ’yan Najeriya za su sake zabar APC saboda sun san irin ta’asar da PDP ta yi a baya.