✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kudin kula da manyan makarantu

Bayanan da suka fito cewa akwai Naira biliyan 43 a asusun kula da manyan makarantun kasar nan na TETFund, wadanda ba a yin komai da…

Bayanan da suka fito cewa akwai Naira biliyan 43 a asusun kula da manyan makarantun kasar nan na TETFund, wadanda ba a yin komai da su, a daidai lokacin ake fama da matsalar gine-gine da kayan more jin dadin rayuwa, wannan na nuni da gurbacewar al’amura da suka dabaibaye harkokin ilimi a kasar nan.
Abin takaici game da wannan rashin tunani ya bayyana ne, a lokacin da Shugaban Hukumar Asusun Kula da Manyan Makarantu na TETFund, Dokt aMusa Babayo ya gabatar da wata makala a gaban taron Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC. Acewar Babayo, manyan makarantu da dama sun kasa cika sharuddan da ake bukata don su samu kudi, wannan shi ne dalilin da ya sanya suka kasa yin amfani da kudin, duk da tsananin bukatar da ake da ita,. Sakamakon haka kudin na nan ajiye a wani asusu da ke Babban Bankin Najeriya (CBN). Dokta Babayo, ya kuma bayana cewa, wani kaso na kudin ana juya shi ne don ya haifar da riba, wadda ake sake mayar da ita cikin asusun. A shekarar 2013, ya ce an samu kudin ruwa na Naira biliyan 18 daga jarin da aka sanya na asusun.
Da yake bayani kan rashin mika kudin,”duk ko wane irin matsin lamba,’ ga makarantun da suka kasa cika ka;idojin, Dokta Babayo ya ce hukumar na bukatar tabbacin cewa za a yi amfani da kudin yadda ya dace, sannan ya ce hukumar asusun na bukatar sa’ido a akn ayyukan da ake aiwatarwa don shawo kan “ingantaccen cin hanci da rashawa” al’amarin da baya bayyana ta hanyar nuni da ajin da ba a gina shi da inganci ba, ta yadda zai iya rushewa, ya haifar da asarar rayuka.
Duk da haka Babayo ya bayyana aniyar hukumar na raba kimanin Naira Biliyan 250 don aiwatar da ayyukan gine-gine da binciken fannonin ilimi a manyan makarantun kasar nan, nan da karshen wannan shekarar, inda ya jajirce kan cewa lallai sai wadanda suka cika sharuddan za su ci gajiyar kudin. Idan suka nuna gazawa, za mu ci gaba da ajiye kudin a Babban Bankin Najeriya, a cewarsa.
Duk da kokarin hukumar Asusun Raya Manyan Makarantun na TETfund, wajen shirya wa manyan makarantun tarurrukan kara wa juna sani kan yadda za su samu kudi daga asusu, hukumomin gudanarwarsu na nuna gazawa wajen bin kadin al’amarin, a cewarsa.
Wannan wani barkwanci ne mara ma’ana, a ce kudin da aka ware don samar da kayan aikin koyarwa, a rika yin amfani da su wajen horar da jami’an gudanarwar manyan makarantu kan yadda za su samu kudi daga asusu, ba tare da an samu kyakkyawan sakamako ba. Lallai akwai bukatar shugabannin makarantun su san muhimmancin tallafin kawo dauki don raya makarantunsu, tare da yadda za su samu kudin.
Halin ko-in-kula da hukumomin gudanarwar manyan makarantun ke nuna wajen samun kudin Asusun tallafa wa makarantun na TETfund, ba wai rashin sani ba ne kana bin da ya dace su yi, ko kuma saboda sarkakiya da tarnaki aikin gwamnati ba. Abin da kawai hankali zai iya dauka wajen bayyana dalilin da ya sa manyan makarantun suka samun kudin tallafin, ya danganta ne kan yadda suka  kashe kudin da aka ba su a baya.Akwai yiwuwar wasu sun yi amfanin biyan bukatun kansu; idan daidaiku ba za su samu ba; to makarantun ba za su ci gajiyar komai ba ke nan. Wannan na nuni da cewa mun samu kanmu a halin koma-baya. Tsare-tsaren Asusun Tallafa wa Manyan Makarantun na TETfund a irin wannan yanayi yana da kyau, kuma kamata ya yi a dore da shi. Abin da kawai ya dace Hukumar bayar da tallafin ta yi, shi ne fito da wani shiri da zai bai wa shugabannin manyan makarantun damar amfani da kudin wajen aiwatar da ayyukan gine-gine da bayar da horo ga ma’aikata, wadanda suka hada da masu koyarwa da ma wadanda ba sa koyarwa.
Wani tsarin da ya dace da asusun hukumar TETfund, shi ne daga lokaci zuwa lokaci, ta rika wallafa sunayen manyan makarantun da suka nuna gazawa wajen cika sharuddan cin gajiyar kudin. Irin wadannan bayanai sai a raba su ga majalisu da hukumomin kula da manyan makarantun, inda su kuma za su bibiyi kadin al’amarin a tsakaninsu da hukumomin gudanarwa na makarantun da al’amarin ya shafa. Sannahn akwai bukatar kungiyoyin malamai da na ma’aikata da na tsofaffin dalibai, su rika bin kadin yadda makarantunsu ke cin gajiyar asusun TETfund. Ayyukan da ake aiwatarwa su ne muhimman al’amuran da ya kamata a sa ido a kai.