✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ku tarar da ni a ruga

Ku tarar da ni a ruga Wani Bafulatani ne ya yiwo canjin kudi tsaba, yana cikin tafiya sai daya ya fado daga aljihunsa. Koda ya ga…

Ku tarar da ni a ruga
 Wani Bafulatani ne ya yiwo canjin kudi tsaba, yana cikin tafiya sai daya ya fado daga aljihunsa. Koda ya ga haka sai ya ce: “Oho, dama kuna tafiya kuke ba ni wahala?” Sai  ya watsar da sauran, ya ce: “Ku tarar da ni a ruga.”
Daga Hafizu Wanka Kano, 09030400620

Mai gadin gawa

Wani mutum ne mai gadin makabarta, sai aka kawo gawarwaki  uku aka aje a dakin ajiye gawa. Da aka zo daukar gawa daya daga cikin ukun, sai ya shiga ya bude musu kofa suka dauka.  Shi kuma sai ya koma ciki, domin ya gyara sauran, a wurin fitowa sai kofa ta rike masa riga. Maimakon ya juya ya ga abin da ya kama rigar, sai ya yi tsammanin ko gawa ce ta rike masa riga. Nan sai ya kama ihu da kururuwa kuma ya ki waigawa ya ga abin da ya kama masa rigar.
Daga Hussaini Sunshine Birnin Gwari, 08032824939

Hawan rakumi

Wani Bahadeje ne ya je wurin wani Malami domin a yi masa fassarar mafarki, ya ce: “Malam na yi mafarkin na hau rakumi.” Sai Malam ya ce masa: “Za ka shiga Aljanna.” Bahadeje ya ji dadi, sai ya ci gaba da cewa: “Ai Malam in gaya maka, har kan tozonsa na je.” Jin haka sai Malam ya ce: “Ka wuce Aljanna, ka shiga wuta.” Sai ya ce: “To, ai da na je sai na zamo kasa.”
Daga Musa Uke Karu, 08051702591

dan baiwa

Wani mahaukaci ne ana duba tsayuwar watan Azumi, babu wanda ya gan shi, sai ya ce: “Laa, ga wata!” Sai aka ce: “Kai, lallai wannan mutumin dan baiwa ne.” Shi kuma da ya ji an yabe shi sai ya ce: “Ku duba nan, ga wani watan can ma, har yau ma ga wani can!”
Daga Sani Ibrahim, 08076231488