Majalisar Wakilai ta nemi Hukumar aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta yi bayani game da shirye-shiryenta na gudanar da aikin Hajjin 2024.
Shugaban Kwamitin aikin Hajji na majalisar, Jafaru Muhammed ya bayyana wa manema labarai cewa ’yan Najeriya na da ƙorafe-ƙorafen dangane da aikin Hajjin 2024 da ke tafe.
Ya ce, “Maniyyata ‘yan Najeriya na kokawa sosai kan irin kuɗaɗen da akai ta neman su bayar domin samun sauke farali, da yawa daga cikinsu manoma ne.
“Muna matukar bukatar NAHCON ta tausaya wa ’yan Najeriya, a yi la’akari da halin da suke ciki, sun biya kuɗaɗen ajiya lokacin da Dala ta na Naira 1000 har ta kai N2000, yanzu farashin Dala ta faɗi, ta sauko zuwa tsakanin Naira 1000 zuwa 1,100 zuwa N1,200.
“Don haka yana da kyau mu duba waɗannan abubuwan, ba wani abu ne mai sarkakiya ba, domin an san farashin kudin aikin Hajji, sufuri da sauran ayyuka.
“Don haka yana da kyau maniyyata su san ko nawa ake kashewa a yanzu, kuma su san nawa ne za a mayar musu canji.
“Mun zauna da Hukumar aikin Hajji ta ƙasa, mun kuma faɗa musu cewa su gaggauta sanar da maniyyata abin da za a dawo musu da shi a matsayin canji, domin su rage waɗansu abubbuwan da ke gabansu.”
Ya ce, wannan dalilin ne ya sa suka aikawa hukumar takardar buƙatar su fito su yiwa ‘yan Najeriya bayani mai gamsarwa domin a daina wannan ce-ce-ku-ce.