Wata kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kano, ta bayar da umarnin a kamo sanannan mawakin siyasar nan, Dauda Kahutu Rarara.
Alkalin da ke jagorantar shari’ar, Ibrahim Sarki Yola ne ya bayar da umarnin kamo mawakin saboda kin bayyanarsa a gaban kotu don kare kansa daga zargin da ake yi masa.
- ’Yan bindiga: Sojoji sun kubutar da mutum 10 a Zamfara
- Zaben Nijar: Namadi Sambo zai jagoraci masu sa ido na ECOWAS
- Fadar Shugaban Kasa ta fara nazarin sake rufe iyakokin Najeriya
Tun da farko kotun ta aike wa Rarara sammaci kan ya bayyana a gabanta ranar 22, ga watan Disambar 2020, saboda tuhumar da ake masa na boye matar aure ba bisa ka’ida ba.
Mijin matar mai suna Abdulkadir Inuwa ne ya shigar da karar yana neman a bi masa hakkinsa a kotun Musuluncin.
Mijin matar na zargin mawaki Rarara da saka matarsa ta aure a bidiyon wakarsa ta siyasa mai taken ‘Jihata, Jihata ce’.
Ya shaida wa kotun cewa an yi wata ba a san inda matar tasa ta shiga ba, don haka ya roki kotun da ta bi masa hakkinsa.