Kotun Koli za saurari shari’o’i da aka daukaka zuwa gabanta na kalubalantar zaben Yahaya Bello a matsayin Gwamnan Jihar Kogi a rana guda.
Daya daga cikin lauyoyin da ake shari’ar da su ya ce Kotun Koli ta sanya ranar Talata 25 ga Agusta domin sauraron daukaka karar.
Lauyan wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya ce kotun ta riga ta aike wa dukkannin bangarorin da ke shari’ar sanarwar zaman.
Dan takatar Jam’iyyar PDP a zaben gwamanan Musa Wada ya shigar da karar ne domin kalubalantar nasarar Gwamna Yahaya Bello na Jam’iyyar APC.
Akwai kuma wasu ‘yan kara guda uku da suka hada da na ‘yar takarar Jam’iyyar SDP Natasha Akpoti da ke neman kotu ta soke zaben saboda zargin magudin da aka tafka. Jam’iyyun DPP da APP kuma na kalubalantar hana su shiga zaben.
A baya Kotun Daukaka Kara ta yi watsi da dukkannin koke-koken ‘yan takarar, ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraron Kararrakin Zaben da ya ba wa Yahaya Bello nasara, bisa hujjar cewa masu karar sun kasa kawo kwararan hujjoji.