✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotun Koli ta tabbatar da daurin shekara 12 da aka yi wa Jolly Nyame

Kotun Koli a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Name, zuwa shekaru 12 a gidan yari…

Kotun Koli a ranar Juma’a ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Name, zuwa shekaru 12 a gidan yari kan laifin rashawa na Naira biliyan 1.6.

Kwamitin mutum biyar na kotun koli wanda babbar mai shari’ar kotun Mary Peter-Odili, ta jagoranta a cikin hukuncin da ta yanke, ta ajiye hukuncin biyan tarar Naira miliyan 495 da kotun daukaka kara ta kakaba wa tsohon gwaman. A zaman kotun da aka yi a cikin watan Mayu na 2018 da Nuwamba 2018 ne aka yanke wannan hukuncin.

A yayin da  take gabatar da hukuncin kotu a kan karar Nyame, Mai shari’a Amina Augie ta ce, ba daidai bane Kotun daukaka kara ta sanya tara akan tsohon gwamnan ba.

Ta ce, duk da haka ta tabbatar da laifin da kuma hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke wa tsohon gwamnan na rage shakarun daurin da aka yi masa a baya daga shekara 14 ta rage zuwa 12.