Babbar Kotun Tarayya da ke Jihar Kano karkashin Mai Shari’a Abdullahi Liman, ta sanya 19 ga watan Yulin 2022, a matsayin ranar soma sauraron rokon soke umarnin da ta bayar na dakatar da gwamnatin jihar daga karbo bashin Naira biliyan 10.
A ranar 1 ga watan Yuli ne, kotun ta dakatar da gwamnatin jihar daga karbo bashin Naira biliyan 10, sakamakon wani roko yin hakan lauyan wadanda suka shigar da karar, Barista Badamasi Suleiman ya gabatar.
- Sunayen kwalejojin kiwon lafiya 26 da gwamnatin Kano ta rufe
- Yadda rashin tsaro ke barazana ga Zaben 2023 a Arewa
Bayanai sun ce, yayin zaman kotun na ranar Juma’a, Lauyan gwamnati, Dahuru Mustapha ya nemi da ta janye umarnin da ta bayar na hana karbo bashin.
Lauyan ya lissafo rashin bin ka’idar shigar da kara da kuma boye wasu muhimman bayanai a matsayin hujjojinsa na neman kotu da ta janye umarnin da ta bayar.
A nasa martanin, Barista Badamasi ya yi kira ga kotu da ta yi watsi da hujjojin Lauyan gwamnati don gudun shiga rudani kan batun da ake magana a kansa.
Wani Dr. Yusuf Isiaka Rabiu ne ya garzaya kotun, inda ya nemi ta dakatar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje da wasu hukumomi na jihar daga karbo bashin Naira Biliyan 10 domin dasa kyamarorin CCTV a wasu sassan jihar.
Gwamnatin ta Kano dai ta yi ikirarin karbo bashin bisa dalilin cewa za ta dasa kyamarorin ne da zummar inganta tsaro a jihar.