✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta dage sauraron bukatar Abduljabbar na sauyin kotu

Kotun Shari'ar Musulunci ta dage shari'ar Abduljabbar zuwa ranar 4 ga Agusta, 2022

Lauyoyin Gwamnati kuma masu gabatar da kara a shari’ar da ake yi wa Abduljabbar Kabara sun yi suka game da rokon da ya yi na a canza masa kotu sakamakon zargin da ya yi wa kotun cewa ba za ta yi masa adalci ba.

Tun dai a watan Yulin bara ne Gwamnatin Jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a kan zargin yin batanci ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam da kuma tayar da hankulan jama’a.

Lauyoyin gwamnatin karkashin jagorancin Barista Suraj Saida (SAN) ya shaida wa kotu cewa babu wata hujja da malamin zai bayar a kan a canza masa kotu har ta amince ba tare da wasu cikakkun hujjoji ba.

Barista Saida Suraj ya shaida wa kotun cewa in har ta amince da canza wa wanda ake kara kotu to fa zai ci gaba da neman a canza masa a can gaba.

Har ila yau masu gabatar da kara sun kafa hujja da wasu shari’o’i da aka yi a kotun daukaka kara wacce kuma ta yi hani ga canjin kotu don bukatar wadanda ake yi wa shari’a.

Sai dai lauyan wanda ake kara Barista Dalhatu Shehu Usman ya roki kotun da ta sanya wata rana domin ya sami cikakken lokacin da zai mayar da martani game da sukar da masu gabatar da kara suka yi akan batun canjin kotun.

Alkalin kotun, Mai sharia Ibrahim Sarki Yola, ya dage shariar zuwa ranar 4 ga Agusta 2022.

%d bloggers like this: