Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci ta Daya da ke Tudun Wada, Zariya, ta yanke wa wadansu magidanta uku daurin zaman gidan yari na shekara daidaya ko zabin biyan tarar Naira dubu bakwai-bakwai da bulala 20 ga kowanensu kan samunsu da laifin yin fyade ga ’yan makarantar firamare masu shekara 9 zuwa 10 da haihuwa.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kaduna ne ya gabatar da karar ta hannun wakilinsa Saje Adamu Yahaya yana tuhumar mutum ukun da laifin yi wa ’yan firamaren fyade. Wadanda ake yanke wa hukuncin su ne Hassan Suleman da Ibrahim Usman da Adamu Audu, dukkansu mazauna Bakin Dogo a Unguwar Tudun Jukun, Zariya a Jihar Kaduna.
Saje Adamu Yahaya ya ce abin da suka aikata laifi ne da ya saba wa sashi na 222 da 117 Final Kod, kuma wadanda ake tuhuma da laifin fyaden dukkansu sun amsa laifinsu.
Alkalin Kotun Mai shari’a Iliyasu Muhammad Umar ya yanke musu hukuncin zama gidan yari na shekara daya ko zabin biyan tarar Naira dubu bakwai tare da bulala ashirin ga kowannensu.
Wakilan Kungiyar Sintiri ta Gyara Kayanka ne suka kama wadanda suka aikata fyaden, kuma sun yi wa Aminiya bayanin cewa Hassan Sulaiman da Ibrahim Usman, su biyun sun tarar wa yariya daya ce (an sakaya sunanta) mai shekara 9, inda idan za ta makaranta sai su tare ta a hanya su yi mata fyade, yayin da Adamu Audu yake yin fyade ga daya yarinyar (an sakaya sunanta) mai shekara 10, kuma yaran duk makarantar firamarensu daya (an sakaya sunan makarantar).
Da yake yi wa Aminiya bayani kan lamarin Sarkin Tudun Jukun Alhaji Jibirin Yakubu ya yi kira ga iyaye su rika kula da kai-komon ’ya’yansu, kuma su rika bin ’ya’yansu bayan su tura su makaranta. Ya shawarci malamai su rika kula da amanar da aka dora musu idan suka lura cewa wani yaro ko yarinya ba ta zuwa makaranta a kan lokaci, su yi kokari sanar da iyayensu abin da suka lura da shi.
Sarkin ya yaba wa kungiyar tsaro ta Gyara Kayanka wadda ke kula da tsaron unguwar inda ya ce al’ummar unguwar su ci gaba da ba su goyon baya kamar yadda aka saba.
Da Aminiya ta tuntubi Kwamishinar Harkokin Mata da Yara da Walwala ta Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Muhammed Baba ta nuna rashin jin dadinta kan hukuncin inda ta ce ya saba wa “Sabuwar dokar fyade musamman sashi na 31 (2) wanda ya ce duk wanda aka same shi da laifin tarawa da karamar yarinya ya aikata laifin da ya saba wa karamin sashi (1), kuma fyade yana karkashin wannan sashi da za a yi masa hukuncin daurin rai da rai,” inji ta. Ta ce karamin sashi na (3) ya ce “In wanda ake tuhuma da fyade a karkashin wannan sashi babu kwakkwarar hujja a kai sai (a) An tabbatar da wadda ake zargin ya kai ko ya wuce shekara 18 (b) kuma da yardar ita yarinyar ce ya yi jima’in. (4) Kuma dukkan wata doka da za a yi amfani da ita ba za ta yi aiki ba har sai an samu kammalallen rahoton likita ko an ga zahirin abin da ya aikata ta hanyar amfani da na’urar zamani da za ta tabbatar da ya aikata fyaden ko bayanan iyayenta ko ita yarinyar da wannan kotu za ta zartar da hukuncin daurin rai da rai a karkashin dokar.