Rahotanni daga kasar Sin na nuni da cewa, an yanke wa tsohon babban mai ba da shawara kan harkokin siyasa na lardin Liaoning, Liu Guoqiang, hukuncin kisa tare da daurin shekaru biyu bayan da aka kama shi da laifin karbar cin hanci.
Kotu ta yanke wa Liu wannan hukuncin ne bayan da ta kama shi da laifin karbar cin hanci na sama da Yen miliyan 352 na kudin kasar, kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 48.
- An kama masu sayar da kayan da Bankin Duniya ya bayar a raba wa dalibai a Kaduna
- ’Yan bindiga sun sace matar tsohon Gwamnan Bauchi
An same Liu da yin amfani da damar mukaman da ya rike wajen amfanar da kungiyoyi da daidaikun jama’a.
Bayanan da kotun ta samu sun ce, mai laifin ya amfani jama’a a harkoki daban-daban wanda ta wannan hanya ya karbi cin hanci.
Kotun ta ce Liu ya tara makudan kudade ta hanyar karbar cin hanci, kuma laifin da ya aikata ya haifar da asara babba ga yankin da ma al’ummarsa.
Ta kara da cewa, Liu ya amsa laifinsa ya kuma yi nadama, kana ya ba da hadin kai wajen dawo da kudaden haramun da ya tara.
(NAN)