✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta wanke tsohuwar ministar kudi, Kemi Adeosun

Kotun ta ce ba a bukatar takardar shaidar kammala NYSC kafin a zama minista

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja ta wanke tsohuwar Ministar Kudi Kemi Adosun daga zargin tana da hannu wajen yin katin shaidar yi wa kasa hidima (NYSC) na jabu.

A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, Alkalin Kotin, Mai Shari’a Taiwo Taiwo, ya ce Adeosun ba ta cancanci shiga wannan shirin ba a lokacin da ta kammala karatu tana da shekaru 22 saboda ita ‘yar kasar Birtaniya ce.

  1. Haihuwa ta yi yawa a sansanonin ’yan gudun hijira — Zulum
  2. Buhari da Osinbajo sun sa wa Janar Farouk anini

“Wadda ake kara ‘yar asalin Birtaniya ce tun daga 1989 zuwa lokacin da ta kammala karatunta a  Jami’ar Gabashin Landan, [don haka] ba ta da damar mallakar shaidar kammala hidimar kasa kamar yadda dokar NYSC ta CAP N8, LFN, 2004 ta tanada.”

Alkalin ya ci gaba da cewa lokacin da ta dawo Najeriya ta haura shekara 30 don haka ba za ta mallaki takardar shaidar kammala hidimar kasa ba.

Mai Shari’a Taiwo ya ce wacce aka yi karar ko waninta ba ta bukatar takardar shaidar kammala NYSC don tsayawa takarar zama dan Majalisar Wakilai ko kuma a nada ta a matsayin minista a Najeriya.

A watan yulin 2018 ne dai takaddama ta barke game da sahihancin takardar shaidar kammala hidimar kasa ta ministar, lamarin da ya sa ta ajiye aikinta a watan Satumban shekarar.

An zargi ministar da yin amfani da takardar shaida ta jabu duk da cewa kafin a nada ta minista ta yi kwamishinar kudi a Jihar Ogun.