✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta tsare barawon Takalma 21 a Kano

Matashin ya saci takalma da darajarsu ta kai Naira dubu 243.

Wata kotun shari’ar musulunci da ke zaune a a Karamar Hukumar Fagge ta Jihar Kano, ta ba da umarnin tsare wani mai suna Umar a gidan kaso, bisa tuhumarsa da laifin satar takalma.

Aminiya ta ruwaito cewa, ana zargin matashin da satar takalma har kafa 21 wanda darajarsu ta kai kimanin Naira dubu 243.

‘Yan sanda ne dai suka gabatar da karar a gaban kotun kan wanda ake zargin da ke zaune a unguwar Kofar Ruwa.

Sai dai Umar ya musanta zargin da ake masa, lamarin da ya sanya Alkalin kotun, Isma’il Muhammad Ahmad ya dage zaman zuwa 9 ga watan Agusta .

Tun da fari dai, dan sanda mai gabatar da kara, Abdul Wada, ya sanar da kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Yuli a Unguwar Goron Dutse.

“Da misalin karfe 3 na ranar 22 ga watan Yuli ne, wanda ake zargin ya balle shagon wani mai suna Sani Abubakar kuma ya saci takalma kafa 21,” a cewar Wada.

Dan sandan ya kuma sanar da kotun cewa lokacin da wanda ake zargin ya shiga hannu, an samu takalma kafa shida a hannunsa.

Laifukan a cewarsa, sun saba wa sashi na 133 na kundin dokar kotun.