✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar wa Abdullahi Sule kujerarsa

Kotun daukaka kara da ke Makurdi babban birnin jihar Benuwe, a yau Talata ta tabbatar da nasarar zaben Injiniya Abdullahi Sule, a matsayin Gwamnan jihar…

Kotun daukaka kara da ke Makurdi babban birnin jihar Benuwe, a yau Talata ta tabbatar da nasarar zaben Injiniya Abdullahi Sule, a matsayin Gwamnan jihar Nasarawa daga jam’iyyar APC.

A zaman kotun da aka yi yau kotun ta watsi da karar dan takarar Gwamnan Nasarawa na jam’iyyar PDP Mista Emmanuel David Ombugadu, ya shigar don kalubalantar nasarar zaben Injiniya Abdullahi Sule na APC da aka yi ranar 9 ga Maris 2019.

Kotun ta amince da sanarwar hukumar zabe INEC ta yin a tabbatar da Injiniya Abdullahi Sule, a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan jihar Nasarawa.