✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta tabbatar da nasarar Kofa a matsayin dan majalisar tarayya

Kotun ta ci tarar dan takarar APC 100,000 kan bata mata lokaci.

Kotun sauraren kararrakin zabe ta ’yan Majalisar Dokoki da ke zamanta a Kano ta yi Allah-wadai da gazawar Muhammad Sa’id Kiru na jam’iyyar APC wajen gabatar da shaidu kan karar da ya shigar kan nasarar Abdulmumini Jibrin Kofa na jam’iyyar NNPP.

Alkalan kotun uku da ke jagorantar shari’ar, Mai Shari’a Ngozi Flora, ta ce takardun da bangarorin biyu suka gabatar a gaban kotun sun nuna Abdulmumini Jibrin Kofa ya yi murabus daga mukaminsa na babban sakataren hukumar gidaje ta tarayya, kwanaki 30 gabanin gudanar da zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

A cewarta, mai shigar da kara ya kasa cika hujojji na tabbatar da cewa an tafka kura-kurai a zaben ba tare da bin dokar zabe ta 2022.

Alkalim ta kori karar tare da jadadda Kofa a matsayin zababben dan majalisa mai wakiltar mazabar Bebeji da Kiru daga Jihar Kano.

Har wa yau, kotun ta ci tarar wanda ya shigar da karar kudi Naira 100,000 kan bata mata lokaci.