Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a Jihar Kano ta ba da umarnin a gudanar da gwajin lafiyar kwakwalwa da kuma kunnen Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.
Hakan dai ya biyo bayan amincewa da bukatar Babban Lauyan Surajo Sa’ida, bayan Sheikh Abduljabbar ya ki cewa uffan a kan dukkan sabbin laifukan da aka karanta masa.
- Dan bindigar da ya yi garkuwa da Daliban Afaka ya shiga hannu
- Daukar makami don kare kai laifi ne —Babban Hafsan Soji
Alkalin kotun, Mai Shari’a Ibrahim Sarki-Yola ne ya bayar da umarnin yayin zaman kotun ranar Alhamis.
Mai Shari’a Sarki-Yola ya ce likitan kwakwalwa daga Asibitin Kula da Masu Tabin Hankali da ke Dawanau a Jihar da kuma liktitan kunne daga Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano ne za su duba malamin sannan su kawo wa kotun rahoton bincikensu.
Sabbin zarge-zarge guda hudun da aka karanta wa Sheikh Abduljabbar dai sun shafi zargin yin batanci da kuma cin zarafin Annabi Muhammad (SAW) yayin karatuttukansa na Jauful-Fara.
Hakan, a cewar masu kara ya saba da tanade-tanaden sashe na 382(b) na Kundin Dokokin Shari’ar Musulunci na Jihar Kano na 2000.
To sai dai alkalin kotun ya ce dogaro da shashe na 278(i) na kundin dokokin ACGL, yin shirun da malamin ya yi na nuna cewa bai amince da dukkan zarge-zargen ba.
Tun da farko dai sai da lauyan da ke kare wanda Abduljabbar, Barista Saleh M. Bakaro ya shaida wa kotun cewa masu shigar da kara ba su da damar janye zarge-zargensu na farko domin su canza su da wasu sabbi ana tsaka da shari’ar.
Amma alkali Sarki-Yola ya ce suna da ikon yin hakan dogaro da sashe 390 (i) na kundin dokokin ACGL na 2015.
Daga nan ne sai lauyan malamin ya bukaci kotun da ta ba su kwafin dukkan zamanta tun daga fara shari’ar domin su daukaka kara, musamman a kan batun sauya sabbin tuhumce-tuhumce da kuma kawo sabbin lauyoyi masu mukamin SAN har guda hudu da gwamnati ta yi, inda ya ce ba su da hurumi a karkashin dokar kotun.
Alkali Sarki-Yola ya amince da bukatar ta su sannan ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa 16 ga watan Satumbar 2021, kuma ya ba da umarnin a ci gaba da tsare Sheikh Abduljabbar a kurkuku har zuwa lokacin.
Sai dai ya ce daukaka karar tasu ba za ta hana kotun ci gaba da sauraron shari’ar ba.
Gwamnatin Jihar Kano ce dai tun a ranar 16 ga watan Yulin 2021 ta gurfanar da Sheik Abduljabbar a gaban kotun bisa zargin aikata sabo da batanci da sauran laifuka.