✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An hana manyan motocin fasinja aiki a Kano

Kotu ta rufe tashoshin manyan motocin fasinja da KAROTA ta kai kara gabanta

Wata babbar kotun majistare dake zamanta a Kano ta dakatar da manyan motocin safa-safa daga hada-hada a jihar har zuwa lokacin da za ta yanke hukunci kan karar da aka shigar a kan haka.

Dakatarwar dai ta shafi tashar da ke New road a unguwar Sabon Gari da ma sauran manyan tashoshi.

Hukuncin dai ya biyo bayan yin kunnen uwar shegu da umarnin Hukumar Kula da Ababen Hawa ta Jihar wato KAROTA na komawa wata sabuwar tashar da ta tanadar musu.

Da take yanke hukuncin, alkaliyar kotun, mai shari’a Rakiya Lami Sani ta ce matakin ya biyo bayan bukatar hakan da hukumar ta KAROTA ta yi a gabanta.

A kunshin karar dai, lauyan hukumar ta KAROTA Mutawakkil Ishaq Muhammad ya bukaci ta dakatar da kamfanoni 15 daga hada-hada a jihar.

Kotun dai ta umarci kwamishinan ‘yan sanda na jihar da ya rufe tashar motar da ke Sabon Gari da ma sauran tashoshin motocin.

Kamfanonin da ake kara da hukuncin ya shafa sun hada da Service Tarzan Motors, Best Way Motors, Landstar Express, Delta Express, Welfare Transport,G.U.O Motors, F.G Onyewe Motors da kuma Godbless Ezenwanta Motors.

Sauran sun hada da Young Shall Grow Motors, Ifeanyi Chukwu Motors, Bonnyway Motors, Chimeze Motors, Gobison Motors, S D. Express da kuma First Tarzan Motors.

Mai Shari’a Rami Lami Sani ta dage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Satumba.