✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta kashen auren miji mai kwankwadar giya

Kotun gargajiya ta Oja-Oba/Mapo a Ibadan ta raba auren Opeyemi da mijinta Josiah Moses da suka shafe shekara 13 suna zaman aure zuwa yanzu, inda…

Kotun gargajiya ta Oja-Oba/Mapo a Ibadan ta raba auren Opeyemi da mijinta Josiah Moses da suka shafe shekara 13 suna zaman aure zuwa yanzu, inda kowanne ya kama gabansa.

Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade ya ce ya yanke hukumcin raba auren ne bayan sauraron bangarori 2 na miji da matar da aka fahimci cewa zai yi wuyar gaske su ci gaba da zama tare.

Uwargida Opeyemi ce ta kai karar mijin nata Josiah da ta roki kotun ta raba aurensu a dalilin kasa daukar dawainiyar gida, musamman kudaden cefane da na makarantar ’ya’yansu guda 3 da kudin hayar gidan da suke zaune da sauran bukatun yau da gobe. Ta shaida wa kotun cewa ita ce take ciyar da dukkansu da abincin kowace rana da daukar nauyin sauran muhimman bukatun abubuwa. Ta ce idan mijin nata ya dawo sai ya kama ta da fada cewa ta zuba masa abinci kadan ba nama.

Matar ta ci gaba da fada wa kotun cewa: “A yayin da abokan mijina Josiah suke gwagwarmayar neman abin da za su kula da iyalansu a kowace rana, shi kuwa mijina yana yin amfani da kudinsa ne wajen kwankwadar giya a kowane lokaci da yake dawowa gida a buge da amayar da giyar da ya shawo da yin fitsarin kwance da auka mani da duka da yawan fada da makwabta.”

 Opeyemi ta ce, “babban kuskuren da na taba yi a rayuwata ita ce auren Josiah da na yi. Wannan ne dalilin da ya sa nake rokon kotu ta raba auren kuma a ba ni damar tafiya da ’ya’yanmu guda 3 domin ci gaba da kula da rayuwarsu.”

Da yake kare kansa, Josiah ya shaida wa kotun cewa, “dukkan abin da ta fadi karya ne, domin ni ne nake yin amfani da kudina da nake mika mata domin kula da bukatun gida da dawainiyar ’ya’yanmu. Ta riga ta bata sunana a idon ’ya’yana da ba su kallona da daraja. A kowane lokaci muka samu sabani da ita sai ta fara yin habaici da zagina a gaban ’ya’yana.”

Bayan raba wannan aure, Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade ya umarci Josiah da ya rika biyan kudi Naira dubu 10 a kowane wata ga tsohuwar matar tasa da za ta yi amfani da su wajen ciyar da ’ya’yan nasu.