Wata babbar kotun Jihar Kaduna ta ki amince wa da bayar da belin wadanda ake zargi da kashe Abdulkarim dan Sanata Bala Ibn Na’Allah, tare da ba da umarnin ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali.
A hukuncin da ta yanke, alkalin kotun, A. A. Bello, wadda ta ki bayar da belin wadanda ake tuhumar, ta bayyana cewa ba ta ga alamun rashin lafiya ga wadanda ake tuhuma ba.
- Babu wanda na kullata a cikin wadanda suka yi takara da ni – Tinubu
- Bayan nasarar Tinubu, Atiku ya shiga tattaunawa da Gwamnonin PDP
Amma ta ce in har bukatar duba lafiyarsu ta taso, kotun za ta ba da izinin kai su asibiti.
Daga nan sai ta dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Yuli don ci gaba da shari’ar.
Tun da farko, lauyan wadanda ake zargin, Nasiru da Salisu wato Mista Kimi Abang, ya roki kotun da ta bayar da belin wadanda ake zargin.
Abang, yayin gabatar da bukatar belin, ya ce ya dogara ne da rahoton rashin lafiya da likita ya rubuta na bukatar duba lafiyar wadanda ake tuhuma.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa wadanda ake tuhumar sun yi wa Abdulkarim fashin kaya da suka hada da waya kirar Samsung, kwamfuta Apple da mota kirar Lexus G5-350 2013 sannan kuma suka yi masa kisan-gilla.
Laifukan, inji mai gabatar da karar, sun saba da sashe na 6 (b), 1 (2) (a) & (b) na Kundin Dokar Mayan Laifuka na Jihar Kaduna.