✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure Shugaban APC da ya mallaki katunan zaben 367 a Kano

Sai dai wanda ake tuhumar ya ce ba shi kadai ya aikata laifin ba.

Kotun Majistare mai lamba 70 a Jihar Kano ta daure Shugaban Jam’iyyar APC na garin Yautan Gabasawa a Karamar Hukumar Gabasawa bisa samunsa da laifin mallakar katunan zabe 367.

Tunda farko ’yan sanda ne suka gurfanar da Aminu Ali a gaban Kotun bisa zarginsa da mallakar katunan zabe na mutane daban daban.

Lokacin da aka karanta masa takardar tuhumar, ya amsa dukkanin laifukan da ake zarginsa da su da suka hada da hadin baki da na mallakar katunan zabe a suka wuce ka’ida.

Duk da cewar ya bayyana wa kotu cewa tare da wasu ya aikata laifin, sai dai har zuwa lokacin da kotun ta yanke hukuncin ba a kai ga kama mutanen ba .

Alkalin Kotun Mai shari’a Faruk Ibrahim Ahmad ya yanke masa hukuncin daurin watanni shida ko tarar Naira dubu 50 a laifi na farko.

Haka kuma yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu ko tarar Naira dubu 500 saboda laifi na biyu ya aikata.

Masu gabatar da kara karkashin jagorancin Barista Bashir Yusuf Tudun Wuzurchi, sun yaba wa kotun bisa wannan hukunci da ta yanke.