✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Kotu ta daure mutumin da ya kashe kaninsa

Wata kotun majistare da ke Kano ta bada umarnin tsare wani mutum mai shekaru 37 a gidan gyaran hali, bisa yi wa kaninsa duka har…

Wata kotun majistare da ke Kano ta bada umarnin tsare wani mutum mai shekaru 37 a gidan gyaran hali, bisa yi wa kaninsa duka har sai da ya mutu.

’Yan sanda dai sun kama Jamilu ne da ke zaune a unguwar Chediyar Kuka a Kano, bisa zarginsa da aikata laifin kisan kai.

Dan Sanda mai gabatar da kara Aminu Dandago ya sanar da kotun cewa da karfe 10:00 na daren ranar 13 ga watan Fabrairun 2022 ne a unguwar ta Chediyar Kuka,  matashin ya rufe kaninsa mai shekaru 30 da duka a sakamakon wani sabani da suka samu.

A cewarsa dukan ya haddasa wa kanin nasa rauni a cikin nasa, har sai da aka kai shi Asibitin na Murtala, in da ya rasu.

Dandago ya ce laifin ya saba wa sashi na 221 na kundin Penal code.

Alkalim kotun dai ya dage karar zuwa ranar 8 ga watan Satumaba 2022.