✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta dakatar da Gwamnatin Kano daga karbo bashin Naira biliyan 10

An hana gwamnatin daukar kowane irin mataki don karbo bashin Naira biliyan 10 daga Bankin Access.

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta dakatar da gwamnatin jihar daga karbo bashi Naira biliyan 10 da ta shirya yi.

Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a A. M. Liman, ta dakatar da gwamnatin Jihar Kano ko wasu ’yan kanzaginta daga daukar kowane irin mataki don karbo bashin Naira biliyan 10 daga Bankin Access.

Aminiya ta ruwaito cewa, gwamnatin Kanon dai ta shirya ciyo bashin ne domin sayen kyamarorin CCTV domin inganta tsaro a fadin jihar.

Sai dai umarnin kotun ya biyo bayan shigar da kara da Kungiyar Kano First Forum (KFF) ta yi gabanta, tana kalubalantar karbo bashin bisa dalilin cewa gwamnatin ta Kano ba ta bi wasu ka’idooji na karbar bashi ba.

Kungiyar KFF ta hannun lauyanta, Barista Badamasi Sulaiman, ta bayyana aniyar Gwamnan Jihar Kano na karbo bashin a matsayin haramtacce saboda ya saba da Dokar karbar bashi ta Ofishin Da ke Kula da Basussuka ta shekarar 2003.

Haka kuma KFF ta ce hakan ya ci karo da Dokar Ma’aikatar da ke da Alhakin Kasafin Kudi ta shekarar 2007 da kuma Dokar Karbar Bashi ta Jihar Kano ta shekarar 1968.

Haka kuma masu karar sun nemi kotun da ta dakatar da Gwamnatin Jihar Kano daga karbar bashin daga Bankin Access ko ma daga kowace irin hanya da sunan samun lamuni.

Wadanda ake karar sun hada da Gwamnatin Jihar Kano da Babban Mai shari’a na Jihar Kano da Kwamishinan Kudi na Jihar Kano da Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano da Bankin Access da Ma’aikatar Kudi ta Kasa da Ofishin da ke Kula da Harkar Basussuka da Maaikatar da ke da Alhakin Kasafin Kudi ta Kasa.

A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sahale wa Gwamnatin Jihar da ta karbo bashin Naira Biliyan 10 daga Bankin Access don sayen kyamarorin CCTV wacce Gwamnatin ta ce za ta sanya a titunan da ke kwaryar birnin Kano.