✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ce a rataye wanda ya kashe abokinsa

Aranar Larabar makon jiya ce  Babar Kotun Jihar Kaduna ta Biyu da ke GRA Zariya, ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Abdullahi…

Aranar Larabar makon jiya ce  Babar Kotun Jihar Kaduna ta Biyu da ke GRA Zariya, ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Abdullahi Ibrahim bisa samunsa da laifin kashe abokinsa mai suna Kabiru Suleiman a watan Disamban shekarar 2011.

Da yake karanta hukuncin, Alkalin Kotun Mai shari’a Kabiru Dabo ya ce bayan kotu ta yi nazarin  laifin da ake tuhumar Abdullahi Ibrahim wanda ya saba wa sashe na 221 na Final Kod. Ya ce “Laifin kisan gilla laifi ne mai karfi, kuma tabbas hukuncinsa na da zafi. Abdullahi Ibrahim wanda ya kashe Kabiru Suleiman a lokacin da ya je wurin da yake aikin gadi cikin Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya domin  karbar kudin mahaifinsa da suka yi amfani da lambar ajiyarsa ta banki, amma sai ya sayo masa lemun kwalba ya kuma sanya maganin barci a ciki inda marigayin Kabiru Suleiman ya sha kuma ya kama barci, sai Abdullahi Ibrahim ya dauko adda da gatari da gora ya buga masa a kai sannan ya sassara shi a kai wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa, kuma ya yi kokarin saka gawar a shadda don ya boye ta.”

Kisan gillar ya auku ne a kan Naira dubu 270 na mahaifin marigayi Kabiru Suleiman, wanda kudin sallamarsa ce daga aiki, inda marigayin ya yi amfani da asusun ajiyar Abdullahi wajen karbar kudin.

Idan masu biye da Aminiya ba su manta ba mun kawo muku  labarin cikakkiyar alakar marigayi Kabiru Suleiman da abokinsa Abdullahi Ibrahim wadanda abokai ne, kuma dukansu daga Karamar Hukumar Ikara da ke Jihar Kaduna suke. Amma duk da haka ya ci amanarsa ya kashe shi a kan kudi, bayan ya kashe shi ya gudu na tsawon shekara guda, daga baya aka kamo shi a garin Kura ta Jihar Kano. Bayan kamo shi ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta hannun lauyanta Barista Jummai Dan’azumi ta shigar da kara a kai, inda aka dauki lokaci ana gudanar da shari’ar.

Bayan sauraron shaidu daban-daban kan kisan ne, aka yake masa hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.