✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ce a ci gaba da tsare matar aure kan zargin kisa

Wata Babbar Kotu a Birnin Tarayya da ke Kubwa a Abuja, ta ba da umarni a  ci gaba da tsare wata matar aure mai suna…

Wata Babbar Kotu a Birnin Tarayya da ke Kubwa a Abuja, ta ba da umarni a  ci gaba da tsare wata matar aure mai suna Rukayyat Abdulkarim kan zargin kashe wani matashi. Matar wadda ke zaman aure a garin Gauraka a Karamar Hukumar Tafa a Jihar Neja, an kama ta ce da kuma gurfanar da ita a gaban kotun kan zargin kashe matashin dan shekara 18 lokacin da ta tunkari mahaifiyarsa da zargin boye mata miji, bayan ta garzaya zuwa gidanta da ke Unguwar Pipe Line a Kubwa a farkon watan Junairun bana.  Matashin ya tare ta a kan ci wa mahaifiyarsa zarafi da ta yi.

Lauyan matar ya bukaci kotun da ta ba da belinta kan dalilan jinkai kasancewar tana tsare a kurkukun Suleja tun lokacin tare da danta mai wata 8 da take shayarwa, baya ga wadansu ’ya’ya biyu da suke tare da mahaifinsu a gida.

Sai dai bayan lauyan ya gabatar da bukatar tun a baya, kotun ba ta samu zaman yanke hukunci a kai ba, kasancewar ta je hutu sai a ranar Talata da ta gabata, inda Mai shari’a K.N. Ogbannaya ta yi fatali da bukatar kan dalilan girman zargin da ake yi mata na aikata kisa.

Haka Mai shari’ar ta ce raunukan da wadda ake tuhumar ta fuskanta na kujewar baki da kuma kafa a yayin rigimar, tuni ta warke bayan an yi mata jinya a baya. Kotun ta kuma yi watsi da bukatar belin a kan dalilin rashin lafiya da lauyan matar ya ce sashin ba da magunguna da ke cikin kurkukun Suleja ba zai iya jinyarta ba, inda Mai shari’ar ta ce dole ne a samu tabbacin haka daga wani asibitin gwamnati maimakon mai zaman kansa da ta ce lauyan ya gabatar.

Mai shari’ar ta bukaci lauyan ya fuskanci kare wadda yake wakilta a kan laifuffuka da ake zarginta mamakon mayar da hankali wajen nema mata beli, sannan ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 12 da kuma 13 ga watan gobe.