Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bayar da belin Sanata Ali Ndume.
Mai Shari’a Okon Abang ya ce ya bayar da belin Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ne bisa la’akari da nagartarsa da kyawun halayensa.
- Arewa ta fi ko’ina hatsari a Najeriya —Sarkin Musulmi
- Masu halin bera sun hana ruwa gudu a gwamnatin Buhari — Ndume
- Yadda Boko Haram ta kashe mutum 93 a rana guda —Ndume
Da yake bayar da belin, Mai Shari’a Abang ya shardanta wa Sanatan kawo mutum daya mazaunin Abuja wanda kuma zai gabatar da shaidar mallakar gida a Abuja.
Mai tsaya masan zai kuma yi rantsuwa cewa ya amince kotun ta kwace abin da zai jinginar mata muddin aka saba sharudan balin.
Ya kuma umarci Ndume da ya hannanta takardar fasfo dinsa ga Magatakardan kotun da kuma bin dukkanin dokokin da kotun ta gindaya masa.
Kotun ta tsare Ndume ne a kurkukun Kuje saboda rashin kawo Abudlrasheed Maina wanda yake fuskantar shari’a bisa zargin karkatsar da wasu kudade.
Maina shi ne tsohon Shugaban Kwamitin Gyaran Fansho na Kasa (PRTT), hukumar da ake zarginsa da karkatar ta kudaden daga nan.
Ndume ya tsaya masa kotun ta sake shi ne bayan ta shardanta dole sai dan Majalisar Dattawa mai ci ya tsaya masa, ya kuma bayar da jinginar Naira miliyan 500 kafin ta ba da belinsa.
Bayan sakin Maina, wanda bai sake halartar zaman kotu ba ake kuma wasar buya da shi, Ndume ya ce ba da son ransa ya karbi belinsa ba.
Zuwa yanzu dai kotun ta bayar da umarni ga jami’an tsaro su nemo Maina duk inda yake su kuma kawo mata shi domin ya girbin abin da ya shuka.