✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kotu ta ba da belin Gwamna Fayose kan Naira miliyan 50

Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas Mai shari’a Mojisola Olatoregun ta ba da belin tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose a shekaranjiya Laraba a…

Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Legas Mai shari’a Mojisola Olatoregun ta ba da belin tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose a shekaranjiya Laraba a kan Naira miliyan 50.

A ranar Litinin da ta gabata ce Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta gurfanar da Ayodele Fayose a gaban kotun,  bisa zarginsa da almundahanar Naira biliyan 30.8, zargin da ya musanta. A ranar Mai shari’a Mojisola ta ba da umarnin cewa Hukumar EFCC ta ci gaba da tsare shi a wajenta.

An gurfanar da Fayose ne tare da kamfaninsa, Spotless Inbestment Limited a gaban kotun, inda aka tuhume shi da aikata laifin almundahana a lokacin da yake rike da mukamin Gwamnan Jihar Ekiti.

Bayan an gurfanar da Fayose, a ranar Litinin lauyansa Kanu Agabi  (SAN) ya  nemi belinsa daga kotun kuma ya bayyana kudirin haka ga lauya mai gabatar da kara.

A yayin da yake mai da martani kan wannan batu na lauyan Fayose, lauya mai gabatar da kara, Rotimi Oyedepo (SAN) ya tabbatar da cewa lallai ya samu bayanin bukatar belin, sai dai yana bukatar kotun ta ba shi lokaci domin ya yi nazari kafin ya ba da amsa a kai.

Daga bisani dai Mai shari’a Mojisola ta dage shari’ar zuwa shekaranjiya Laraba, domin a saurari batun belin, kuma ta ba da umarnin a ci gaba da tsare tsohon Gwamnan a wajen EFCC. Bayan sake hallara ne, sai aka ambato batun belin, inda ta amince da ba da belin.