Wata kotu ta yanke wa ’yan dabar Shila Boys da suka addabi Jihar Adamawa da kwacen waya hukuncin daurin shekara bakwai da rabi a gidan yari ba tare da zabi ba.
Kotun Majistare da ke garin Yola ta yanke wa shugaban kungiyar ’yan dabar Shila Boys din da yaransa uku hukuncin ne bayan sun amsa cewa aikinsu ne kai wa mutane hari su yi musu kwacen wayoyi da kuma dukiyoyi.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Japhet Ibrahim Basani, ya ce matasan masu shekara 19 zuwa 25 sun aikata laifi a karkashin sashe na 60 da na 283 na kundin hukunta laifuka na jihar, kuma sun fitini musamman mazauna garin Yola.
A ranar Laraba, 11 ga Agusta, 2021 ne ’yan Shila Boys din suka shiga hannu bayan sun yi wa wani dan banga da ke haya da babur mai kafa uku kwacen waya da kudi a unguwar Doubeli da ke garin na Yola.
Dan bangar, wanda ya ba da shaida gaban kotu, ya ce daya daga cikin matasan ne ya tsayar da shi cewa zai kai shi Bachure, daga baya sai wasu ’yan Shila Boys uku, ciki har da shugabansu mai shekara 25, suka hau babur din suka fara kai masa hari.
– ‘Ni ma dan uwa ne’
Da ya ga haka sai ya nuna musu cewa ai shi ma ‘Dan Nawawu’ ne —wato daya ne daga cikinsu.
Jin hakan sai suka bar kai masa farmaki, amma suka kwace wayarsa ta N3,000 da kuma kudi N7,000 sannan suka kyale shi ya wuce.
Da ya tafi sai ya yi maza ya sanar da abokan aikinsa, su kuma ba su bata lokaci ba wurin bin sawun Shila Boys din, kuma suka cafko su.
Dan sanda mai gabatar da kara, Kabiru Abubakar, ya gabartar wa kotun karin shaidu da suka tabbatar da abin da ya faru, sannan alkali ya yanke hukuncin daurin shekara bakwai da wata shida a kan kowanne daga cikin matasan ba tare da ya ba su zabi ba.
Sai dai ya ce duk wanda bai gamsu da hukuncin ba, daga cikin masu karar da wadanda aka yanke wa hukuncin, yana da damar daukaka kara.