A karon farko tun daga lokacin da kasar nan ta koma tsarin dimokuradiyya a shekarar 1999, kowane daga cikin manyan ’yan siysar da ke Kano: Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da Malam Ibrahim Shekarau da Dokta Abdullahi Umar Ganduje, su ukun sun shiga filin dagar siyasa da tunnin samun nasara ga dan takarar da kowannensu ya tsayar da kuma bukatar son shafe tarihin sauran mutum biyun daga siyasar jihar.
Dukkanin mutannen nan uku su ne suka mulki jihar tun daga shekarar 1999 zuwa yau, inda kowanansu ya yi mulki hawa bibbiyu. Wato shekaru takwas-takwas.
- Canjin kudi: Gwamnonin APC sun yi wa Aso Rock tsinke
- Sojoji sun dakile ’yan bindiga, sun ceto mutum 30 a Kaduna
A yanzu haka kuma kowannensu yana da dan takararsa da ya sanya a cikin tseren son mulkar jihar, inda suke burin ya zama shi ne ya fara kafa tarihin samun nasarar zabe ga dan takararsa.
Wannan dai shi ne karo na farko da za a yi zabe a haka, inda suke a mabambantan jam’iyyu.
A lokutan baya, an samu cewa biyu daga cikinsu ne ke haduwa su yaki daya amma a yanzu lamarin ya canza, inda Ganduje shi ne yake jagorantar Jam’iyyar APC, Injiniya Kwankwso ke jagorantar Jam’iyyar NNPP, sai kuma Malam Ibrahim Shekarau da ke jan ragamar Jam’iyyar PDP.
Tsayar da ’yan takara
Kafin Ganduje ya tsayar da mataimakinsa, Dokta Naisru Gawuna a matsayin dan takarar gwamnan, sai da ya yi ta neman sulhu, kasancewar akwai wasu da suka nuna sha’awar takarar kujerar gwamnan; Yayin da ya zama abu mai sauki ga Kwankwaso wajen sake tsayar da Abba Kabir Yusuf duk da cewa akwai wadanda ba su ji dadi ba.
Sai dai ga Shekarau da kuma jam’iyyarsa ta PDP, rikicin da ya janyo Kwankwaso ya fita daga jam’iyyar ya yi tsamari har ma ana ganin ya shafi takarar jam’iyyar a zaben gwamna.
Har zuwa karshen watan Disamba, Sadik Wali, wanda da ne ga tsohon Ministan Harkokin kasashen Waje, Aminu Wali, shi ne ya zama dan takarar jam’iyyar.
Aminu Wali da Shekarau suna tare inda suka so su rike akalar jam’iyyar a hannunsu tare da korar jama’ar Kwankwaso da suka rage a jam’iyyar wato tsagin da Sagagi ke shugabanta.
Sai dai biyo bayan hukuncin Bababar Kotun Tarayya a watan Disamba wanda ya ayyana Mohammed Abacha a matsayin halastaccen dan takarar gwamanan a jam’yyar, sai Wali da Shekarau suka koma baya duba da cewa Abacha ya fito daga tsagin Sagagi.
Sai dai ba kamar Ganduje da Kwankwaso ba, hanyar da Shekarau ya biyo ta samun nasarar kafa gwamnati a Kano tana da sarkakiya, duba da rikicin gida da ya mamaye jam’iyyar domin ya komo jam’iyyar ne a karshen bara bayan sauya sheka da ya yi daga APC da kuma dan zaman da ya yi tare da Kwankwaso a Jam’iyyar NNPP.
Har yanzu Shekarau da Wali suna fatan hukuncin kotu ya canza yadda dan takarasu zai dawo a matsayin dan takarar jam’iyyar da doka ta amince da shi.
Nasiru Gawuna
Gawuna wanda shi ne dan takarar APC wanda kuma Mataimakin Gwamna ne a halin yanzu, ba a san shi da mummunar alaka da sauran ’yan siyasa ba.
Gawuna tsohon Shugaban karamar Hukumar Nassarawa ne a lokacin Gwmantin Shekerau na shekara takwas.
Haka kuma a shekarar 2011 Gwaman Kwankwaso ya nada shi Kwamishinan Ayyukan Gona.
Har ila yau a shekarar 2015 lokacin da Ganduje ya karbi mulki daga Kwankwaso ya yi masa tazarce kafin daga bisani ya mayar da shi ya zama mataimakinsa bayan Farfesa Hafiz Abubakar ya yi murabus.
A shekarar 2019 Ganduje ya kara tafiya da shi a matsayinsa na mataimakinsa bayan an sake yin zaben.
Shaharar Gawuna
Haka kuma abin da ya faru a lokacin zaben 2019 ne ya kai Gawuna ga matsayin siyasar kasar nan bayan hotunansa inda ya shiga motar ’yan sanda ya karade kafafen sadarwa na zamani.
Abin da ya faru ya hada da karbar sakamakon zabe a lokacin zabe inda shi da Murtala Garo wato dan takarar mataimkainsa kuma tsohon Kwamishinan Kanansn Hukumomi a lokacin, inda suka shiga wurin da ake karbar sakamakon zabe, inda aka zarge su da kawo tsaiko a harkar.
Abin da suka yi ya kawo tsaiko a wajen bayyana sakamakon zabe a cibiyar inda wadansu matasa wadanda ake zargin ’yan Jam’iyyar PDP ne suka yi kokarin kai wa shugabannin biyu hari.
Sai dai ’yan sanda daga baya sun bayyana cewa ba kama Gawuna da Garo suka yi ba, illa kawai sun fitar da su ne daga wurin da ake hayaniya.
Wannan abin da ya faru da jam’iyya mai mulki a kasa da kuma zarge-zargen da ke bin shugabanta da kuma wasu tsare-tsare na gwamnatin da ya kasance mutum na biyu a cikinta ya janyo wa dan takarar matsaloli duk da irin dimbin nasarorin da ya samu a matsayinsa na Kwamishinan Ayyukan Gona da kuma kasancewarsa Mataimakin Gwamna da kuma matakin da ya taka a matsayinsa na Shugaban Kwamitin Kar-ta-Kwana na yaki da cutar COVID-19, abin da ya janyo wa jihar samun nasara a wanann fannin.
Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf dan takarar Jam’iyyar NNPP ya shiga zabe ne da tunanin kwato ‘kujerarsu da aka sace’.
Ya sha fadin cewa shi ya ci zaben shekarar 2019 sai dai an hana shi shiga gidan gwamanti saboda sanarwar da aka bayar cewa zaben bai kammala ba tare da kuma sake yin zabe ba.
Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida-Gida suna ne da ya yi fice a Kano a shekarar 2019 lokacin da ya fito a Jam’iyyar PDP don kalubalantar Gwamna Ganduje wanda kuma ake ganin shahara ta uban gidansa kuma surikinsa malaminsa na siyasa ta shafe shi.
Abba Gida-gida wanda tsohon Kwamishina Ayyuka ne a Gwmanatin Kwankwaso, ma’aikatar da ta gudanar da ayyukan da suka canja Jihar Kano a lokacin mulkin Kwankwason daga shekarar 2011 zuwa 2015.
A kundin da ya fitar na ayyukan da zai yi a Jihar Knao idan an zabe shi mai shafi 70, ya ba banagren ilimi da lafiya muhimmanci tare da kuma jaddada ayyukan da Kwankwasiyya ta yi a jihar.
Ko wannan zai isa Abban ya kwace mulki daga jam’iyya mai mulki? Hakan ya zama abin tatataunawa a wajen al’umma musamamn ma harkar kudi da ake ganin jam’iyya mai mukli na da shi, inda shi kuma Kwankwaso ya raba kafa wajen neman wani mukamin a matakin kasa.
Amma baya ga manyan jam’iyyun guda uku akwai kuma wasu jam’yyun da suma suke fatan samun wanan kujera ta gwaman.
Sauran ’yan takara
Malam Sha’aban Ibrahim Sharada wato dan majalisar wakilai kuma tsohon hadimin Shugaabn Kasa Muhammadu Buahgri wanda a kwanan nan ya fice daga Jam’yyar APC bayan ya rasa tikitin takarar gwamna, yana ta kokarin nema wa kansa suna a wajen matasa.
An yarda cewa Sha’aban Sharada ya yi rawar gani wajen sama wa Jam’yyar APC kuri’u masu yawa musamman ma a Karamar Hukumar Birni wanda hakan ya kawo mata nasara a jihar.
Sauran ’yan takarar kamar su Bashir I. Bashir na Jam’iyyar Labour Party da Salihu Tanko Yakasai na Jam’iyyar PRP da Malam Ibrahim Khalil na Jam’iyyar ADC da Bala Gwagwarwa na Jam’iyyar SDP — wadanda dukkaninsu suka bar Jam’iyyar APC a kwanan nan ko kuma suke da wata damuwa da jam’iyya — dukkaninsu suna sa rai za su sami nasara a zaben.
Sai dai masu sharhi kan al’amuran yau da kullum suna ganin cewa in dai ba an sami cim ma wata yarjejeniya tsakanin wadannan ’yan takara kafin ranar zabe ba, nasarar da za su samu a lokacin zaben zai zama ya rage wa jam’iyya mai mulki ta APC dubban kuri’un da ya kamata ta samu ne.
Masu sharhin siyasa suna ganin cewa akwai yaki babba a tsakanin manyan ’yan siyasar nan uku a jihar.
Sai dai duk da haka akwai dama ga sabbin ’yan siyasa kamar su Sharada, wadanda suke tunanin za su yi wa tsaffin ’yan siyasar nan ritaya ta hanyar samun sakamako mai ban mamaki a lokacin zabe.