✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Super Eagles ya sabunta kwantiraginsa

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF ta sanar da cewa ta cimma matsaya da mai horar da ‘yan wasan kungiyar Super Eagles ta Najeriya kan sabunta…

Hukumar Kwallon Kafar Najeriya NFF ta sanar da cewa ta cimma matsaya da mai horar da ‘yan wasan kungiyar Super Eagles ta Najeriya kan sabunta kwangiraginsa.

Shugaban hukumar, Amaju Pinnick ne ya sanar da hakan a shafinsa na tiwitta, inda ya ce, “ina farin sanar da ku wace Hukumar NFF da kocin Super Eagles Gernor Rohr sun kammala duk wata yarjejeniya. Don haka zai ci gaba da zama kocin Super Eagles. Mun amince da kwarewarsa, kuma muna da tabbacin zai daga martabar kungiyar ta Super Eagles.

“Yanzu sai mu mayar da hankali kan neman gurbin shiga Gasar Kofin Nahiyar Afirka da Kofin Duniya. Wannan ya zama dole, kuma Koci Rohr ya san da hakan. Kamar yadda Ministan Wasanni ya fada, babu daga kafa a wadannan bukatun.”

Shi dai wannan yarjejeniyar da aka cimma, ta kawo karshen lokaci da aka dauka ana kai-koma a kan makoyar mai horar da ’yan wasan.

Shi dai Rohr mai shekara 66, dan asalin kasar Jamus ne da ya taba horar da kungiyar Bordeaux ta Faransa har ta kai ga zuwa wasan karshe na Gasar Kofin UEFA, inda kungiyar Bayern Munich ta lallasa ta da ci biyar da daya a wasanni biyu da aka buga. Sannan ya taba kasancewa Darakta Wasanni na kungiyar Frankfurt ta Jamus. Sannan kuma ya horar da kungiyar Nantes ta Faransa.

Haka kuma, kocin ya horar da kasashe irinsu Guenea da Nijar da Burkina Faso.

A lokacin da yake taka tamaula, ya kasancewa dan wasan bayan kasar Jamus, sannan ya yi wasa a kungiyoyi irinsu Bordeaux da Bayern Munich da sauransu.

Gernor Rohr ya yi kokari matuka wajen kawo sabbin ’yan wasa, musamman zaratan matasa da suke wasa a kasashen waje, sai dai wasu suna ganin bai cika son amfani da ’yan wasan da suke wasa a gasar Firimiyar Najeriya ba.

Ga sanarwar Shugaban NFF Amaju Pinnick: