✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kocin Kano Pillars ya ajiye aikinsa

Kocin ya zargi kungiyar da kin biyansa albashi na tsawon watanni biyar.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars, Emmanuel Lionel Soccoia ya ajiye aikinsa, bayan karya wasu ka’idoji da suka shafi kwantaraginsa.

Lionel ya ajiye aikinsa bayan karbar aikin watanni biyar da suka gabata, tun watan Oktoban shekarar 2020.

Tsohon kocin kungiyar Black Leopards da ke Afrika ta Kudu, ya bayyana rashin cika masa wasu alkawura da ke kunshe a yarjejeniyarsa da Kano Pillars da kuma yi masa katsalandan cikin aikinsa a matsayin dalilan da suka sanya shi ajiye aikin horas da kungiyar.

Lionel ya ce yanzu haka yana bin kungiyar Kano Pillars albashin watanni biyar da yawunsu ya kai Dalar Amurka dubu 25.

Kazalika, ya yi wa kungiyar fatan alheri tare da fatan za su biya shi kudaden da yake bi na tsawon watanni biyar da ya yi yana aiki.

Hakazalika, ya koka kan gazawar da kungiyar ta yi wajen sama mishi takardar izinin zama domin aiki a Najeriya kamar yadda doka ta tanadar, abin da ya sa ofishin jakadancin kasarsa ta Faransa ya nemi ya koma gida, kasancewar ci gaba da zamansa a Najeriya ya saba ka’ida.

Sai dai jami’in hulda da kafafen yada labaran kungiyar ta Pillars Rilwanu Idris Malikawa, ya musanta zargin kocin mai murabus na cewar ana yi masa katsalandan.