✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace sarakunan gargajiya su rika murabus idan sun tsufa?2

A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya…

A wasu kasashe, sarakunan gargajiya sun fito da salon yin murabus suna nada ’ya’yansu a gadon sarauta tun suna raye, Sarkin katar da wata sarauniya a Swiziland da kuma wani sarki a kasar Beljiyom, duk sun yi murabus, suka nada magadansu tun suna da rai. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace sarakunanmu na gargajiya su yi koyi da wannan salon? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu kamar haka:

Abu ne mai kyau su yi murabus
– Musa Yakubu
 Alhaji Musa Yakubu Yagarmawa: “Gaskiya ya dace su yi koyi da abin da want ton basarake na katar ya yi, da ya sauka tun wuri ya ba dansa mulki saboda mafi yawancinsu ka ga tsufa ya kama su kuma shekarunsu sun yi yawa saboda haka ya dace su rika sauka suna ba ’ya’yansu.”