✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace a takaita yawan jam’iyyu zuwa biyu a Najeriya?3

Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita…

Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kacal, a yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya dace a bar su da yawa, domin al’umma su samu zabi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kadai ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

Jami’iyyu biyu sun fi dacewa – Sani Bello

Sani Bello Afiyawai: “Na fi sha’awar tsarin jam’iyyu biyu saboda haka ya fi kawo hadin kai a tsakanin al’ummar kasa da kuma kawo karancin jayayya a lokacin kamfe da kuma zuwa kotu bayan an yi zabe. Amma tsarin jam’iyyu masu yawa na kawo yawaitar rarrabuwar kai ne kawai da kuma rudar da masu zabe, wanda jam’iyya mai mulki ke cin gajiyarsa.”