✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko ya dace a takaita yawan jam’iyyu zuwa biyu a Najeriya?2

Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita…

Idan ana batun al’amuran siyasa a Najeriya, musamman tun daga 1999 zuwa yau, akwai jam’iyyu masu yawa. Wasu na ganin cewa ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kacal, a yayin da wasu kuma ke ganin cewa ya dace a bar su da yawa, domin al’umma su samu zabi. Abin tambaya a nan shi ne, ko ya dace a takaita jam’iyyun zuwa biyu kadai ko kuwa? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kuma ga ra’ayoyinsu:

A samar da jam’iyyu biyu kadai
– Ahmad Hassan
Ahmad Hassan Muhammad Deidei: “A ra’ayina, amfani da tsarin jam’iyyu biyu shi ya fi dacewa da yanayin Najeriya saboda shi zai fi mana sauki wajen rarrabe jam’iyyu a lokacin zabe amma tsarin jam’iyyu masu yawa na rudar da jama’armu, musamman ma na karkara; wanda a wani zubin; a maimakon su zabi jam’iyyar da suke so sai su zabi wadda ba su kauna saboda yawan jam’iyyun ko rashin iliminsu ko karancin fahimta ba za ta ba su damar rarrabewa ba.”