✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko tiririn kwamfuta na da illa ga lafiya?

Shin ko tiririn da ke fitowa daga na’urar laptop yana da illa ga lafiya? Domin ni nakan dora a cinyata amma wani abokina ya gani…

Shin ko tiririn da ke fitowa daga na’urar laptop yana da illa ga lafiya? Domin ni nakan dora a cinyata amma wani abokina ya gani ya ce za ta iya illa. Ko akwai kamshin gaskiya a zancen?

Amsa: Hakika akwai kamshin gaskiya a wannan batu, domin kowa ya tabbatar cewa na’urorin zamani na laturoni suna fitar da dimin zafi na lantarki, da ma na batiri idan suna da shi, haka nan akwai masu aiki da harkar sadarwa wato maganadison radiowabe, su ma suna fitar da tiriri na su na daban. To idan aka yi la’akari da wannan kwamfuta da ka yi magana, wato kwamfutar cinya ko laptop, za ka ga kusan ta hada komai na wadancan nau’ukan tiriri, domin akwai na wuta in a jone ta ke, akwai na batir, akwai kuma na maganadison sadarwa idan aka kunna mata Bluetooth ko intanet wato wifi.

Sai dai ba kamar yadda a da aka rika yayatawa cewa irin wadannan na’urori (musamman ta wayar tafi-da-gidanka) suna kawo daji, ba haka abin yake ba, tunda har yanzu ba a ga wanda aka tabbatar su suka ja masa ciwon daji ba. A’a suna dumama jiki ne kawai, kuma idan dumamar ta faru a wurin da ba a so ba, to za a iya samun matsala. To a jikinmu musamman mu maza akwai wani wuri da ba ya son zafi ko tiriri mai dimi na tsawon lokaci, wadannan wurare sune maraina, kuma sai aka yi rashin sa’a wannan karamar kwamfuta kusan a daidai saitinsu tiririn laptop ke sauka na tsawon lokaci.

Wasu masu binciken kimiyyar lafiyar mafitsara a kasar Amurka a shekarar 2004 sun wallafa kasida akan tabbacin cewa na’urar laptop za ta iya yi wa maniyi da halittun da namiji masu ajiye ruwan maniyin illa. Wannan bincike ya ce wannan na’ura na iya daga tiririn maraina da maki kusan uku a ma’aunin Celsius (3ºC) bayan awa daya kadai, wanda zai iya tashi idan aka kara dadewa. Kuma wadannan kwamfutoci da suka yi amfani da su sabbi ne fil, domin wadanda suka tsufa sun fi fitar da tiriri mai karfi. Su nasu kwamfutocin tiririnsu ya karu da maki tara (9ºC). Da aka kwatanta da saka matsattsun kaya da zama wuri guda sai aka ga yanayin dimin wurin yana karuwa ne kawai da maki biyu (2ºC) a cikin awa daya, wanda ke nuna saka matsattsun kaya ko wando ma na da illa ga lafiyar namiji.

Akwai hanyoyin kariya daga wannan matsala ganin cewa a yanzu da yawan samari wadanda ma ba su taba aure ba, na amfani da wannan na’ura a kan cinya. Da yake na’urorin kan tebur su ma suna fitar da tiriri ba a nuna cewa za su mana illa sosai ba tunda ba sa taba jikinmu. Don haka kenan idan mutum za yi amfani da na’urar laptop sai ya sai mata karamin teburi, wato dai ta bar jikinsa yayin da yake amfani da ita. Masana suka kara da cewa a cire wayar wutar caji idan ana amfani da ita, a yi amfani da batir kawai, domin a rage yawan tiririn, kada a rika aiki da duka biyun (tiririn lantarki da na batir). Sa’annan idan ta kama dole sai an dora a cinya saboda gajiya da sauransu to dole ne a sayi faifan kiyaye tiriri wato radiation shield a wurin masu sayar na na’urar.

 

Mene ne amfanin daddawa ga lafiya?

Daga Nasir Kainuwa, Hadejia

 

Amsa: Ita daddawa da kalwa a ke yi, wato wani nau’in wake da ake cewa locust beans a turance. To shi ma wannan wake kamar sauran nau’ukan wake yana da amfani ga jiki, wato suna da sinadarai ne masu gina jiki. Da ma ai kusan dalilai biyu ne ke sa a sa daddawa a miya, kara dandano da neman abu mai gina jiki, kada a ci miya lami. Kenan ko ba a sa nama a miya ba aka sa daddawa za a iya samum amfani sinadari mai gina jiki. Wasu ma za ka ga wake dai da muka sani dafaffe shi suke watsawa a miyar yauki duk dai saboda a samu irin wancan amfani.

Ita matsalar daddawa ita ce wajen sarrafa kalwar wato wajen tsima ta. A da dai akan ce duk wanda ya ga yadda ake tsuma wannan wake sai ya yi tunani kafin ya ci, saboda ba hanyoyi ba ne masu tsabta, amma ba mu sani ba a yanzu ko matan zamani sun iya tsima ta cikin tsabta.

 

Ni na kasance ina da son atile. Mene ne amfaninsa ga lafiyar jiki?

Daga Tijjani A., Kano

 

Amsa: E, atile wani dan itace ne mai lafiyayyen maiko da sinadaran bitamin iri. An fi kiransa da zaitun din Afirka saboda kamanceceniya da ‘ya’yan zaitun, amma dandanonsa kamar na ‘ya’yan fiya mai maiko (abocado) kuma ana kyautata zaton yana da abubuwan amfani na cikin zaitun da fiya din kamar su bitaman na rukunin A da E da sinadaran potassium da magnesium. Shi mansa maiko ne mai amfani wanda ke iya tsane maikon jiki maras amfani, kamar dai man zaitun da man kifi.

 

Wace irin illa kankara ke kawowa ganin yadda wasu ke sa ta a abubuwan shansu kamar fura da nono da lemukan gida?

Daga Garba Sabiyola, Gashua

 

Amsa: A’a kankara ba ta da wani illa idan dai da ruwa mai tsabta aka yi ta. Wato dai kafin ka sayi kankara ya kamata ka tambaya ko da wane irin ruwa aka hada ta. Idan dai da gurbataccen ruwa aka yi ta ne to fa duk wasu cutukan ruwa irinsu kwayoyin kwalara da na typhoid da kwayayen macizan ciki za su iya daskarewa da ransu, amma da sun narke su farfado. Wato dai sanyin kankara babu tabbacin zai kashe wadancan kwayoyin cuta.

 

Mece ce alakar olsa da rake ne? Domin ni ina yawan shan rake, amma bayan na gama ina yawan gyatsa

Daga A.A.G., Kano

 

Amsa: Babu wata alaka tsakaninsu, domin mai olsa zai iya shan rake lafiya lau, kuma rake ba ya sa olsa din. Sai dai idan ka sha rake da yawa tare da hadiyar iska yayin shan raken za ka iya samun yawan gyatsa, tunda ita gyatsa ai iska ce a tumbin cikinka kake fitarwa.