Hukumar gudanarwar kamfanin siminti na BUA ta ce ko sisi kamfanin bai kara ba a kan farashin kowane buhun siminti.
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da kakakin kamfanin, Sunday Ogieva ya fitar ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce, “Kamfanin siminti na BUA na nesanta kansa daga dukkan wani kari da aka yi a kan farashin siminti.”
Ya ce sanarwar ta zama wajibi kasancewar kamfanin ya jima yana karbar korafe-korafe kan karin N300 a kan farashin buhun siminitan kamfanin.
“Muna sane da cewa bukatar siminti ta karu matuka, la’akari da irin yadda ake samar da adadin da ba ya iya wadatar da jama’a.
“Amma duk da haka, mun yi amanna da cewa karin farashin ba zai zama maslaha ba, musamman ma a irin wannan lokacin.
“Mun hakikance cewa dukkan wani kari a kan muhimman kaya ba zai kai Najeriya ga tudun mun tsira ba, musamman a wannan lokacin da kasar ke kokarin murmurewa daga kalubalen tattalin arzikin da annobar COVID-19 ta haifar,” inji shi.
Kamfanin ya kuma yi “kira ga dillalanmu da su tabbatar da cewa ba su kara kudin ba da nufin cin kazamar riba.”