✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko sisi ba mu biya ba kafin a sako daliban Kankara – Gwamnatin Katsina

Ya ce gwamnatin ta yi amfani da hanyoyi na kwarewa wajen tabbatar da cewa ko kwarzane wani daga cikin yaran

Sakataren Gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Mustapha Inuwa ya ce gwamnatin jihar ba ta biya ko sisin kwabo ba a matsayin kudin fansa kafin a sako dalibai 344 da aka sace daga makarantar sakandire ta Kankara a jihar.

Mustapha, wanda ya bayyana hakan a tattaunawarsa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a Katsina ranar Talata ya ce duk da yake an sha wahala wajen kubutar da yaran, amma ko sisi ba a biya ba.

Ya ce gwamnatin ta yi amfani da hanyoyi na kwarewa wajen tabbatar da cewa ko kwarzane wani daga cikin yaran bai samu ba kafin a sako su.

Sakataren gwamnatin ya ce, “Sabanin wasu jita-jita da ake yadawa cewa gwamnati ta biya Naira miliyan daya a kan kowanne dalibi kafin a sako shi, amma ko sisi ba mu biya ba.

“Duk da yake mun fuskanci kalubale mai yawa, mun tabbatar ba a sami ko da yaro daya ya rasa rayuwar sa, muna murnar cewar dukkansu sun koma gida sun sadu da iyayensu lafiya,” inji shi.

Daga nan sai ya yabawa kokarin Gwamnatin Tarayya da jami’an tsaro kan namijin kokarin da suka yi wajen tabbatar da kubutar da yaran.

Idan dai za a iya tunawa, ’yan bindiga sun sace dalibai 344 a Makarantar Sakandiren Kimiyya da Fasaha ta garin Kankara a dakunan kwanan su a ranar 11 ga watan Disambar 2020, kafin daga bisani a sako su bayan shafe mako daya a tsare.