“Ina rokon `yan kungiyar Malaman Jami`o`in kasar nan, da s u sake duba matsayin da suka dauka a cikin halin da a ake ciki, wanda kuma yake kawo koma baya a cikin harkokin tafiyar da jami`o`inmu, wanda ya tilasta wa dalibai ba sa jami`o`insu yau watanni hudu.”
“Muna rokonsu da su musanya bacin ransu da kishin kasa. Da ya zama wani abu na daban zuwa yanzu da gwamnati bata sauraren koke-kokensu ko kuma ba ta da aniyar ta amince da yarjejeniyar da suka kulla da ita, mun ri ga mun yi alkawarin cewa dukkan yarjejeniyon da muka kulla za mu cika su. Har yanzu suna bukatar su amince cewa ba wani sashe na fannin tattalin arzikin kasar nan da yake aikin da ya cancance shi.”
Wadannan kalamai na daga cikin jawabin da shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan ya gabatar a karshen makon jiya a garin Ado-Ekiti babban birnin jihar Ekiti a lokacin da yake bikin bude Kwalejin koyon ilmin injiniya na jami`ar Afe Babbalola, yana mai gargadin cewa bai kamata a sadaukar da makomar kasar nan ba akan yajin aiki, abin da ya ka iya kawo mummunan koma bayan ci gaban kasar nan ta fannoni daban-daban. Don haka ya roki shugabannin kungiyar Malaman jami`o`in kasar nan, wato ASUU da su sake duba matsayin da suka dauka, yau kusan watanni hudu ke nan, al`amarin da ya haddasa miliyoyin dalibai, wadanda suke manyan goben kasar nan ba sa zuwa jami`o`insu.
Wannan yajin aikin `yan kungiyar ta ASUU da aka fara tun ranar 1 ga watan Yulin da ya gabata, a yau yana da kwanaki 117, ya samo asali ne, bisa ga bukatar kungiyar ASUU, na lallai gwamnatin tarayya ta fara aiwatar da yarjejeniyar da suka sanya hannu akai a shekarar 2009, yarjeniyar da ta kunshi fara bada Naira biliyan 100, a shekarar 2012, don inganta harkokin koyo da koyarwa a daukacin jami`o`in kasar nan, wato kamar gine-gine da kayyakin ayyukan koyarwa da bincike. Kuma a shekarar 2013, da 2014, a samar da Naira biliyan 400, duk dai don ganin kyatatuwar wadancan fannoni. amma har zuwa lokacin da suka fara yajin aikin babu labarin an fara aiwatar da waccan yarjejeniya.
Wata bukatar da yarjeniyar ta kunsa, ita ce biyan Malaman jami`o`in wasu kudin alawus-alawus dinsu, kudin da lokacin da aka fara yajin aikin sun kai Naira biliyan 80. amma har zuwa lokacin da suka fara yajin aikin babu labarin an fara aiwatar da waccan yarjejeniya.
Fara wannan yajin aiki na ASUU ke da wuya, kamar yadda aka saba a kasar nan akan kowane yajin aiki sai gwamnatin tarayya ta shiga tattaunawa da su, amma dai kai ka ce tamfar ba`a ma tattaunawar, bare a ce ga wani haske da aka samu na kawo karshen al`amari, duk da kuwa gwamnatin tarayyya ta yi tayin bayar da Naira biliyan 100, don fara aiwatar da ayyukan koyo da koyarwa da kuma Naira biliyan 30, don rage bashin alawus-alawus din Malaman. Tuni gwamnatin tarayya ta raba wadancan Naira biliyan 30, ga jami`o`in. ta kuma ba Hukumar kula da jami`o`im kasa wato NUC waccan Naira biliyan 100, da yanzu take shirye-shiryen rabawa ga jami`o`in.
Jami`ar Ilorin da ta raba wadancan kudin alawus-alawus ga Malamanta, tuni kungiyar ta ASUU, ta zargeta da neman karya mata tsarin yajin aikin. Abin da ASUU ke so shi ne kada wata jami`a da ke cikin wannan gwagwarmaya da ta sa gaba da ta ma kalli wadancan kudi, bare ta karbesu, har sai gwamnatin taryya ta biya mata bukatunta kaf.
Kamar yadda shugaban kasa ya fadi a Ado-Ekiti, ba wani fannin tattalin arzikin kasar nan da a yau yake samun irin kudaden da yake bukata don tafiyar da ayyukansa, matsayin da `yan kungiyar suka fi kowa sa ni, amma don masu iya magana kan ce ruwan da ya dakeka shi ne ruwa, shi ya sanya suka dage akan lalle sai an biya masu bukatunsu a tashi daya.
Ba wanda zai yi musu akan cewa fannin ilmi babban fanni ne, mai matsayin gaske akan ci gaban kasa da mutanenta, don kuwa dukkan kasashen duniya da a yau ake cewa sun ci gaba walau akan kere-kere ko kiwon lafya ko gine-gine, koma shi kanshi ilmin, ba da kome suka kai ga fagen da suka kai din ba, da ya wuce ilmin da mutanen kasar suke da shi.
A maganar da ake ciki ba jami`a daya ta kasar nan da take cikin jerin sunayen zaratan jami`o`in kasashen duniya, duk kuwa da duniya, an yi ittifakin kasar nan ita ce kasa ta shidda a jerin kasashen duniya masu arzikin man fetur, fetur din da da arzikinsa kasashe irinsu Saudiyya da Kuwait da Iraki da Iran da Libya da sauransu suke kyautata rayuwar mutanensu, ta fannin ilmi da kere-kere, amma mu muna baya akan ingantaccen ilmin Firamare, kar ka yi batun na Sakandare da na sauran makarantu.
Tunda aka fara wannan yajin aiki, duk wanda ya isa ya yi roko ga kungiyar ta ASUU, da ita kanta gwamnatin tarayya na a daidaita ya yi, har an kai matsayin da yanzu matsin lambar da ya hada da zanga-zangar kungiyoyin dalibai ko rokon Iyayen daliban da na sauran shugabannin al`umma ya fi karkata akan kungiyar ta ASUU, na ta yi wa Allah, ta yi wa ManzonSa da ta koma bakin aiki, ko `ya`yan talakawa su koma jami`o`insu. A irin wannan lokaci ake ta kukan tabarbarewar tarbiya tsakanin matasan kasar nan takai inda takai, amma dai shiru kake ji wai an aiki Bawa garinsu.
Ina ga lokaci ya yi da shugabannin kungiyar ta ASUU, za su saurari irin wadannan kiraye-kiraye, idan ba so suke ba, yajin aikin nasu ya zarta na wanda aka yi na watanni shidda a shekarar 1996, a zamanin gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha, gwamnatin da marigayi Dokta Mahammad Tahir Liman ya yi wa Minisatan Ilmi.