Ya zuwa yanzu dukkan jam`iyyun da za su fafata cikin babban zabe shekarar 2015, sun samu cimma wa`adin Hukumar Zabe ta kasa wato INEC, wajen mika mata jerin sunayen `yan takararsu da za su tsayar a cikin wadanan zabubbuka idan Allah Ya kaimu. Mika sunayen ya biyo zabubbukan fitar da gwani da jam`iyyun suka yi, wanda duk da sun wuce, amma dai sun bar baya da kura a kusan dukkan wadancan manyan jam`iyyu biyu a jihohi daban-daban, musamman a jihohin da aka yi hadaka, bayan kafa sabuwar jam`iyyar APC, ta hanyar hadewar da rusassun jam`iyyun ACN da ANPP da CPC da wani bangare na APGA suka yi a bara waccan, da aniyar su tunkari jam`iyyar PDP, mai mulki da gwamnatin tsakiya tun a shekarar 1999, da aka dawo mulkin jamhuriya ta hudu, a babban zaben bana, don masu iya magana kan ce “Kisan baki sai taro”.
Alal misali a Jihar Nassarawa, tuni tsohon Minisatan Yada Labaran kasar nan a gwamnatin jam`iyyar PDP, Mista Labaran Maku, wanda a `yan watannin baya ya sauka daga kan mukaminsa ya yi wa jiharsa ta Nassarawa tsinke, inda ya shiga takarar neman mukamin gwamnan jihar, a jam`iyyar su ta PDP,ya bar jam`iyyar, ya canja sheka zuwa jam`iyyar APGA. Mai yiwuwa dama Mista Maku yana da alaka da jam`iyyar APGA, a dalilin tsohuwar shugabarsa marigayiya Farfesa Dora Akunyili, wadda a daidai irin wannan lokaci a shekarar 2011, ta ajiye mukaminta na Minista ta canja sheka zuwa jam`iyyar APGA, ta kuma samu takarar neman mukamin dan Majalisar Dattawa a Jihar Anambara, zaben da ba ta yi nasara ba.
Bayan kafuwar babbar jam`iyyar adawa ta APC ce wasu gwamnonin biyar na jam`iyyar PDP, ciki kuwa har da Gwmnan Jihar Kano, Dokta Rabi`u Musa Kwankwaso (sauran gwamnonin su ne na jihohin Kwara da Sakkwato da Adamawa da Ribas) suka bar jam`iyyarsu suka koma sabuwar jam`iyyar APC. Komawar da ta ba su dama bisa ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin sabuwar jam`iyyarsu suka karbe jagorancin jam`iyyar ta APC a jihohinsu, bisa tanade-tanaden Kundin tsarin mulkin jam`iyyar, da ya tanadi cewa inda duk gwamna yake shi ne jagoran jam`iyyar a jiharsa. Wannan dama ta sanya a jihohin Kano da Sakkwato, tsofaffin gwamnoninsu, wato Malam Ibrahim Shekarau da Alhaji Attahiru Bafarawa, wadanda da su aka kafa APC, ala tilas suka bar jam`iyyar ta APC, suka koma PDP (wannan canjin sheka ta sanya aka yi wa Malam Shekarau Ministan Ilmi). Tsofaffinn gwamnonin biyu, tun a wancan lokaci sun yi zargin cewa, ba za su samu adalci ba daga gwamnonin jihohinsu ba, don haka suka ce ba su ga wurin zama ba a APC din.
Tun a wancan lokaci na canjin shekar wadancan gwamnoni, a Jihar Kano, jahar da ta gaji siyasar bangarori ake batun bangaren PDP Kwankwasiyya da na Janar Buhari na tsohuwar CPC, (bangarori biyu da suka fi karfi a hadakar ta Kano) da bangaren ANPP da ita kanta ACN, ta yadda komai za a yi a cikin tafiyar da siyasar jihar a karkashin hadakar sai kowane bangare ya nemi lallai a raba a ba shi nasa kason. Koda da aka yi zabubbukan majalisun kananan hukumomin jihar 44, a ranar 17 ga watan Mayun bara sai da batun neman a yi raba daidai din ya kawo farraka. Da dadi, ba dadi, haka dai aka yi zabubbukan bangaren Kwankwasiyyar ta tashi da kusan komai.
Yanzu ma batun da ake ciki ke nan akan mukamin dan takarar gwamnan jihar da na mataimakinsa, inda mutane hudu da suka hada Dokta Abdullahi Umar Ganduje daga bangaren Kwankwasiyya da Alhaji Lawan Jafaru da dan Majalisar tarayya Alhaji Sulaiman Abdurrahaman Kawu Sumaila (`yan bangaren Janar Buhari) da Alhaji Usman Alhaji shi kuma mai zaman kansa. Daf da za a fara kada kuri`a Alhaji Kawu da Alhaji Usman Alhaji suka bada shelar sun janye takararsu, suna kuma mara wa Dokta Ganduje baya, don haka takara ta rage tsakanin Dokta Ganduje da Alhaji Lawan Jafaru, inda bayan an kada kuri`a, Dokta Ganduje ya samu nasara da gagarumin rinjaye.
Ba wai `yan hadakar ba kawai, hatta mutanen jihar da suke da ra`ayin jam`iyyar APC din, sun yi tsammani bangaren Kwankwasiyyar zai dauko kodai dan Majalisa Kawu ko kuma Alahji Lawan Jafaru ko Alhaji Usman, kai koma wani daga dai bangaren `yan hadakar ya ce shi zai rufa wa Dokta Ganduje baya. Amma ina sai kawai kwatsam jama`ar jihar da ma na kasa suka ji labarin `yan Kwankwasiyyar sun dauko daya daga cikinsu, wato jagoran siyasar karamar Hukumar Gwale kuma Malami a Jami`ar Bayero Kano, Farfesa Hafizu Abubakar ta ce shi zai rufa wa Dokta Ganduje baya a cikin zaben na 28 ga watan Fabrairun bana in Allah Ya kaimu.
Waccan sanarwa ta kara yamutsa hazon siyasar jihar, da har ta kai ga wasu na tambaya, anya kuwa shugabannin da suke jagorancin APC a Jihar Kanon (`yan Kwankwasiyya) suna fatan jam`iyyarsu ta kai bententa a cikin zabubbukan; anya kuwa Kwankwason ba so yake ya kashe jam`iyyar ba? Tuni dan Majalisa Kawu da magoya bayan Janar Buhari, irin su Abdulmalik dan Bilki Kwamanda sun nemi lallai uwar jam`iyyar ta sa baki wajen kawo gyara, ko kuma su dauki matakin da ba zai haifar wa jam`iyyar a jihar da mai ido ba, a zabubbukan masu zuwa. Yayin da shi kuma jagoran jam`iyyar APC din a Jihar Kano, kuma gwamnan jihar, Dokta Rabi`u Kwankwaso ya tsaya hakan da su kam sun yi adalci, har ma an ruwaito shi yana lallashin `yan hadakar da cewa hakuri ya kamata su yi, yana mai hanzarin cewa haka siyasa ta gada idan mutum bai samu abin da yake so a yau ba, gobe zai samu.
Mai karatu, wannan shi ne halin da jam`iyyar hadaka ta APC ta ke ciki a Kano, halin da ya kai matsayin da tuni Alhaji Ibrahim dan`azumi Gwarzo Kamfen Darakta na Alhaji Usman Alhaji, ya bada shelar su suna nan tare da Dokta Ganduje, yayin da ake jin Alhaji Lawan Jafaru zai iya zaman cikin APC, ko don Janar Buhari. Da wannan danbarwa a cikin APC a jihar Kano jama`a suke tambayar “Bisa ga rikicin da ta shiga, ko jam`iyyar APC za ta iya kai bentanta a jihar Kano.”
Ko rikici zai bar APC ta kai bententa a Jihar Kano?
Ya zuwa yanzu dukkan jam`iyyun da za su fafata cikin babban zabe shekarar 2015, sun samu cimma wa`adin Hukumar Zabe ta kasa wato INEC, wajen…