“Baba (Obasanjo) ya wuce dan jam`iyya kawai. Shi wani garkuwar kasar nan ne, shugaba kuma mai kirkira, wanda ya samar da dukkan cibiyoyin kasar nan a yau tun daga kan shugaban kasa zuwa gwamnoni, wadanda suke `ya`yansa da ya samar. Don haka idan uba ya yi fushi `ya`yansa, ba abin da za mu ce da shi, sai mu ce a yi hakuri.” Wasu daga cikin kalaman Alhaji Sule Lamido Gwamnan Jihar Jigawa ke nan a ranar Talatar da ta gabata, jim kadan bayan shugabancin jam`iyyar na kasa da wasu gwamnonin PDP, sun kammala wani taro da shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan a fadar shugaban da ke Abuja.
Taron ya biyo bayan kusan sa’o’i 24, da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo a wani abu mai kama da almara ko wasan kwaikwayo, inda ya sa shugaban mazabarsa ta unguwa ta II, karamar Hukumar Abeokuta ta Arewa, Alhaji Surajudeen Oladunjoye da ya keta katin shi (Obasanjo) na zamansa dan jam`iyyar PDP, a gaban `yan mazabarsa su kusan 350, kuma akan idanun duniya, yana kuma dariya. Shugaban mazabar, ya ja ayarin magoya baya ne zuwa gidan Cif Obasanjo da aniyar su ji daga gare sa irin yadda dangantaka a kullum take kara tsami tsakaninsa da shugaban kasa Dokta Jonathan, har ya ke kwancewa shugaban kasar da jam`iyyarsu ta PDP zane a kasuwa.
A yayin keta katin PDP, Cif Obasanjo ya fadawa mutanen mazabar ta sa cewa a zamansa da dan kasar nan ba ya bukatar a ce sai yana dauke da katin jam`iyya zai iya furta ta albarkacin bakinsa akan irin halin da kasar take ciki da kuma neman yadda za a gyara. Ya ce ba ya bukatar zama dan kowace jam`iyya daga wannan rana, yanzu ya zama Dattijon kasa, dadin dadawa in ji shi muddin yana tare da mutanen mazabarsa, me kuma ya ke nema akan sai yana dauke da katin wata jam`iyya.
daya-da-daya, manazarta harkokin siyasa sun tabbatar da cewa, ba wai a kasar nan kadai ba, a duniya kaf ba a taba samun wani wanda ya ci moriyar jam`iyyarsa irin yadda tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ci ba, amma kuma da ya tashi fita daga cikinta ya yi mata wannan yankan kauna a idanun duniya, ta hanyar sa a keta katinsa na zama dan jam`iyyar, sannan kuma ya bada shelar ya barta haihata-haihata. A dai wannan tafiyar ta jamhuriya ta hudu Cif Obasanjo shi ya fi kowane dan kasar nan amfana da wannan mulki na dimokuradiyya. Mutumin da yake zaman gidan jarun akan daurin rai-da-rai, amma Allah cikin ikonSa ya samu `yancinsa, sannan kuma wadanda suka isa suka sa shi gaba suka ce sai ya dawo ya shugabanci kasar, a zaman shugaban farar hula bayan kusan shekaru 16, sojoji na mulki.
Wannan dawowa karo na biyu akan karagar mulki ta Cif Obasanjo (bayan mulkin soja da ya yi tsakanin shekarun 1976, zuwa 1983, da ya mika wa gwamnatin farar hula mulki), ita ta ba shi damar ya sake mulkin shekaru takwas, inda ya yi wa`adin mulki zango biyu (1999 zuwa 2007). Bayan ya ka sa samun damar yin TAZARCE ne, ya dauko marigayi Alhaji Umaru Musa `Yar`aduwa ya hada aurensa da shugaba Jonathan, inda ya mika masu mulki a shekarar 2007, bayan mutuwar `Yar`aduwa ne (wanda aka yi zargin dama ba shi da cikakkiyar lafiya), tsohon shugaban kasar a zaben 2011, ya sake tsayawa tsayin daka ya tabbatar da cewa, sai Shugaba Jonathan ya sake tsayawa zabe, don ya kammala wa`adin zangonsu na biyu shi da marigayi shugaban kasa `Yar`aduwa.
Ko kusa Gwamna Sule Lamido bai yi karya ba, da ya ce kusan dukkan wanda ke shugaban kasa ko gwamna a yau, Cif Obasanjo ya yi sanadiyyar hawansa karagar mulkin a cikin tafiyarsu ta jam`iyyar PDP. Wannan karfin iko da tsohon shugaban kasa Obasanjo ya ga ya kara yi da kuma irin tarihin da yake da shi na yin katsalandan cikin harkokin tafiyar da gwamnati tun bayan da ya bar kan karagar mulki a karon farko a shekarar 1979, hakan ta sa Shugaba Janar Sani Abacha da ya kasa daure katsalandan din Obasanjon, ya kama shi a shekarar 1993 da tuhumar yunkurin juyin mulki, ya kuma hukunta shi da daurin rai da rai.
Daf da Cif Obasanjo zai kammala zangonsa na biyu a shekarar 2003, bayan ya fahimci yunkurinsa na TAZARCE ya ci tura, sai ya sa aka gyara tanadin kundin tsarin jam`iyyarsu ta PDP, da yake batun nada shugaban Kwamitin Amintattun jam`iyyar ya kasance sai wanda ya taba shugabancin kasa a inuwar jam`iyyar zai iya rike wannan mukami. Wancan gyara ya ba shi damar yana kammala wa`adin mulkinsa, ya dare akan waccan kujera. Amma abinka da harkar mulkin dimokuradiyya shekaru kusan uku bayan Shugaba Jonathan ya zo kan karagar mulki, sai shi kuma ya yi amfani da na sa karfin mulkin ya sa aka canja waccan shedara ta kundin tsarin mulki jam`iyyar, ta koma kamar yadda ta ke a da, wato kowane dan jam`iyya zai iya rike wancan mukami. Sannu a hankali kuma shugaba Jonathan, yana kara mike kafa, yana kuma kawar da dukkan mutanen Cif Obasanjo, walau daga kan mukamin jam`iyya ko na gwamnati tun daga sama har kasa.
Haka aka yi ta wasan buya tsakanin tsohon shugaban kasa Cif Obasanjo da dansa shugaba Jonathan, ta yadda idan tsohon shugaban kasar ya fito a bainar jama`a ya soki shugaba Jonathan da gwamnatinsa akan yin sakacin tafiyar da mulki, musamman akan sukurkucewar matakan tsaro da cin hanci da rashawa da karuwar rashin ayyukan yi da batun fatara da talauci da suka yi katutu a tsakanin `yan kasa a mulkin shugaba Jonathan, shi shugaba Jonathan bai fitowa kai tsaye ya mayar masa da martini, amma zai sa mukarraban gwamnatinsa su mayar masa, shi kuma ya bi ta karkashin kasa ya sadu da Cif Obasanjo don ya shawo kansa. Haka aka yi ta wannan ‘zaman doya da manja’ tsakanin manyan biyu, har ta tura takai bango, inda aka jiyo Shugaba Jonathan yana bayyana wasu tsofaffin shugabannin kasar nan da cewa wasunsu, tamfar `yan tasha ne, maganar da ake zargi da Cif Obasanjo ya ke.
Yanzu dai tura ta kai bango tsakanin Cif Obasanjo da dansa shugaba Jonathan, kamar yadda na fadi tun farko, duniya, tagansu a rana, kai karewa ma da karau Cif Obasanjo na fada wa mutanensa na kusa da na nesa da sauran `yan kasa, yanzu ba ya tare da jam`iyyarsa ta PDP da dan takararta na neman shugabancin kasa a zabubbukan bana. Abin tambaya anan shi ne Ko Cif Obasanjo zai saurari lallashin da jiga-jigan tsohuwar jam`iyyarsa ta PDP zasu yi masa, da ya dawo jam`iyyar, koda a cikinn wannan dan lokaci da ya rage na a yi zabubbukan banan? Ko kusa daga yadda Cif Obasanjo ya husata bana jin zai amince ya dawo cikin jam`iyyar ta PDP. Ficewar da wasu na hannun daman shugaban kasa suke cewa ya yi ne don ya ka sa cimma burinsa na yadda zai rinka juya shugaba Jonathan. Ni a waje na a wannan karon Cif Obasanjo ya zama cikakken dan kishin kasa, wanda ya gani ya yi magana don a gyara, an ki gyarawa ya fice, sabanin wasu masu fada a ji na kasar nan da kodai suke jin tsoron maganar ko kuma suka zama Zalwajahaini. Allah Kai mana maganinsu da `yan kanzaginsu.