A makonnin da suka gabata aka fara bayyana faduwar farashin danyen man fetur, ta yadda zuwa yanzu farashin ya fado daga Dalar Amurka $110, zuwa kasa da $72. Wannan ita ce faduwa mafi muni da farashin ya yi tun cikin watan Agustan 2010. Akwai kuma alamar ba nan farashin zai tsaya ba. A irin wannan hali kasashe masu arzikin man fetur da ke cikin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur wato OPEC, wadanda suka dogara kusan kacokan akan kudin shigar su daga man fetur din, har sun fara kokawa da bayyana irin tsare-tsare da suke jin za su kaisu ga gaci, akan annobar karancin kudi da za su fuskanta. kasashe da ke cikin kungiyar ta OPEC sun hada da Aljeriya da Saudiyya da Iran da Kuwait da katar da Libya da Najeriya da Iraki da Hadaddiyar Daular Larabawa da Benizuwela.
kasashe irin su Saudiyya da Kuwait da makamantansu da suka dade cikin iya dora tsarin tattalin arzikin kasashensu akan irin na kasashen da suka ci gaba, musamman akan fannin masana`antu da inganta ayyukan Noma da kiwo, yi shelar sun shirya tsaf don tunkarar dukkan mummunan mawuyacin yananin da faduwar farashin ka zo da shi. Ya yin da kasashe irin su Iran da Iraki da Binuzuwala da kasar nan, suka fara kame-kame akan irin matakan da za su dauka, ta yadda za su iya tsallake wannan siradi da Allah kadai Ya san lokacin da za a tsallake shi. Faduwar farashin man, har ta fara tilasta wa wasu kasashe fara karya darajar kudaden kasarsu da kansu, kamar yadda babban Bankin kasar nan ya bada shelar karya darajar Naira akan Dalar Amurka daga N155 zuwa N165 akan kowace Dalar Amuka. A kasuwar bayan fage kuwa farashin Dalar yana neman dosar N185 akan kowace Dala daya. Dadin dadawa irin wadannan kasashe da ake bi basussuka za su ci gaba da samun matsalar biyan basussukan da ake binsu, bisa ga karewar kudaden nasu da kuma irin yadda za su samu koma baya cikin samun kudaden shigarsu bisa ga faduwar farashin man..
A `yan kwanakinnan duk inda ta samu damar magana ana ta jin Minista mai kula da tsarin tattalin arzikin kasar kuma Ministar Kudi Dokta Ngozi Okonji Iweala, tana bayyana wasu daga cikin matakan da kasar nan za ta dauka don rage radadin da annobar faduwar farashin man fetur din take tafe da su. Ta fadi cewa gwamnati za ta duba sanya haraji akan wasu abubuwan jin dadin rayuwa kamar jiragen sama da na ruwa da giyar nan ta Shamfe (Champagne) da wasu masu hannu da shuni na kasar nan suke amfani da su. Ta ce hikimar wannan haraji shi ne masu hannu da shunin su kara dandana irin mawuyacin halin da aka shiga, sannan kuma su nauyaya aljihun gwamnati. Wani batun da ta tabo, wanda masana tattalin arzikin kasa suke ganin yana da kamar wuya shi ne irin yadda ta ce za su ci gaba da toshe kafofin da ake sama da fadi da kudin gwamnati, tare da inganta yadda ake tara kudaden shiga na cikin gida da waje.
Akwai kuma wasu matakan tsuke bakin aljihun gwamnati da sai a farkon shekara mai zuwa za a tabbatar da fara aiki da su, kamar janye sassaucin farashin man fetur, janye sassaucin da kugiyoyin kwadago na kasar nan wato NLC da TUC suka sha alwashin za su yake shi, har sai inda karfinsu ya kare. Masana harkokin zirga-zirgar jigaren sama ma na da ra`ayin zai yi matukar wuya gwamnati ta iya tilasta wa Kamfanoni da masu jiragen sama na kashin kansu, su rinka biyan haraji a kan jiragen su. Masanan sun yi nuni da cewa ai Dokar 2006, ta kula da zirga-zirgar jiragen sama ta yi tanadi akan karbar harajin Dalar Amurka $3,000, ga masu zirga-zirgar cikin gida da kuma Dalar Amurka $4,000 ga masu tafiye-tafiyen kasashen waje a duk lokaci da za su tashi, amma Kamfanonin da masu jirage ba sa biya, karshe ma dai suka ce wannan takaddamar tana kotu.Masanan sun kuma ce ta wannan haraji kadai kasar nan za ta iya samun Dalar Amurka $12 biliya duk shekara.
A duk lokacin da kasar nan ta shiga irin wannan hali, ba abin da ke zo mani a zuciya, sai shekarun 1972, bayan kammala yakin basassar shekaru uku, lokacin da shugaban kasa Janar Yakubu Gowon yake fadi da babbar murya cewa “Kudaden shiga ba matsalar kasar nan ba ce, matsalar kasar, ita ce yadda za ta kashe su.” A wancan lokaci kudin man fetur suna kidima masu mulki, masu mulkin da suka kasa yi wa tattalin arzikin harsashin da yake shi ne na kafa masana`antu da ci gaba da habaka harkokin noma da kiwo, wanda da kudinsu aka samu arzikin da aka fara tono man fetur din. .
Don haka daga lokaci zuwa lokaci gwamnatocin da suka biyo baya irin na farar hula na shugaba Alhaji Shehu Shagari da ta shugaba Janar Ibrahim Badamasi Babangida, duk suka shiga irin wannan annoba ta faduwar farashin man fetur, wadda ta sa suka bullo da nasu tsare-tsaren na tada komada irin na SAP. Tsare-tsaren da akasari ba su kai ga nasara ba, saboda barin bida baya da aka yi na gyara wancan kuskure na gwamnatin Janar Gowon, wanda har yanzu akansa ake tafiya.
Ita kanta gwamnatin farar hula ta wannan zamanin ta bullo da nata tsare-tsaren ganin habakar tattalin arzikin kasar nan, musamman tsarin nan na bube ajiyar wasu kudade da aka samu daga rarar farashin man fetur, sama da abin da aka kayyade a cikin kasafin kudi, amma kamar yadda Minista Ngozi ta fadawa mutanen kasa, gwamnonin jihohi su suke matsawa wancan asusu lamba da a debo a raba, al`amarin da ya kai fagen asusun da ke da sama da Dalar Amurka $9 biliyan, a watan Disamban 2012, amma yanzu ta ce bai wuce Dalar Amurka $4biliyan ba.Yanzu maganar da ake da tun tafiya bata yi nisa ba wasu gwamnonin sun fara kokawa da irin koma bayan da suke samu daga Asusun kasa, koda a rabon arzikin watan Oktoban da aka yi a watan da ya gabata, an ruwaito Gwamnan Jihar Binuwai Dokta Gabriel Suswan yana kokawa akan cewa N2.5 biliyan, jiharsa ta samu, alhali albashi kadai yana lakume N3biliyan. Yanzu maganar da ake ma`aikatan jihar suna yajin aiki akan rashin albashi.
Mai karatu, ka ga ke nan kasar nan da mutanenta musamman na arewacinta za su ci gaba da zama cikin fatara da talauci, baya ga ta rashin tsaro da ake fama da shi, kuma abin bakin cikin shi ne, gwamnatoci ba wasu matakai na ba-sani-ba-sabo ba za su dauka, kamar sa wancan haraji da yaki da cin hanci da rashawa da ya addabi kasar nan tun daga sama har kasa, bare kuma su yi kokarin tallafawa muhimman hanyoyin nan da suke habaka tattalin arzikin kowace kasa ta bunkasa, irin na Masana`antu da Makamashi da ayyukan noma da kiwo. karshe abin Allah Ya kiyaye, haka wannan mawuyacin lokaci zai zo ya wuce, mutanen kasa su jikkata rashin ayyukan yi da dama suka yi katutu, su kara ta`azzara, bisa ga Masana`antu da za a kara rufewa, musamman a wannan lokaci da mahukuntn da za su zuba idanu akai ga nasara suke ta fafutikar ganin sun ci zabe ko ta halin kaka. Allah Ka ba mu ikon zaben shugabannin da za su cece mu da kasar nan baki daya.