✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko jam’iyyar APC za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya?4

Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki…

Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kan batun kuma ga abin da suka fada:

Hakan zai samar da kyakkyawar alkibla
– Muhammadu Bello
Alhaji Muhammadu Bello Sagera: “Ko shakka babu, hakan zai samar wa siyasar kasarmu kyakkyawar alkibla, domin Najeriya ta kama hanyar samun tsaftataccen yanayi ta fuskar siyasa saboda duk wani abu da ka sani na duniya, idan babu kishiya to ba za a samu ci gaba nakwarai a ciki ba. Saboda haka samar wa jam’iyyar PDP babbar kishiya irin wannan jam’iyyar ta hadin kan ’ya’yan jam’iyyun adawa babbar nasara ce kuma ci gaba ne kwarai da gaske, ta fuskar ci gaban kasa da kuma ainihin samar wa siyasar kasar nan kyakkyawar alkibla da sauran kasashe za su yi koyi da mu; muddin shugabannin jam’iyyun da suka hadu har Allah Ya taimake su suka gano irin wannan kyakkyawar dabara, suka shirya har suka fito da wannan jam’iyya mai amsa murya guda a kasar nan.