✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko jam’iyyar APC za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya?

Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki…

Alhaji Umaru Gosulo P.Z.Ta tabbata dai jam’iyyar APC ta samu rijista a Najeriya, wanda haka ya sanya ta zama babbar jam’iyyar adawa da jam’iyyar da ke kan mulki ta PDP. Abin tambaya a nan shi ne, ko sabuwar jam’iyyar za ta iya kawo sauyi ko kuma za ta iya canja alkiblar siyasar Najeriya? Wakilanmu sun tattauna da mutane daban-daban kan batun kuma ga abin da suka fada:

Za ta canza siyasar Najeriya – Umaru Gosulo

Alhaji Umaru Gosulo Pz. Zariya: “kwarai kuwa, sabuwar jam’iyar APC za ta canza siyasar Najeriya. Dalili a nan shi ne, har in aka ce wannan sabuwa jam’iyya ta APC ta kafa gwamnati, to jama’ar Najeriya gaba xaya za su canza daga inda suke, domin yanzu siyasar ta shiga ruxani. Hange mutanan da suka kirkire ta dukkansu an san irin jagorancin da suka yi a kasar nan. ACP, tun da ta sami rijista a matsayinta na babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, mu mun shiga sabuwar jamhuriya a Najeriya.”