✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ko a Makka!

Wani Basakkwace ne ya dawo gida daga Legas, inda ya je ci-rani, shi ne sai ya tara abokansa yana ba su labarin irin iskanci da…

Wani Basakkwace ne ya dawo gida daga Legas, inda ya je ci-rani, shi ne sai ya tara abokansa yana ba su labarin irin iskanci da shegantaka da rainin da Yarabawa ’yan Eriyaboyis ke yi musu. Cikinsu akwai wani mai suna Barau, sai ya ce wa abokin nasa: “Idan za ka koma Legas, ni kuwa zan bi ka domin idan sun yi iskanci zan rama maka.” Abokin ya ce masa: “A’a Barau, mutanen nan fa shegu ne na gaske!” Barau ya ce: “Shegantakarsu ta samun wuri ce, duk ranar da suka hadu da ni ta zo karshe!” Haka suka tafi Legas, da suka shiga bas sai kwandasta ya ce su biya kudin mota, shi kuwa Barau ya ce ba zai biya ba. “Me ya sa ba za ka biya kudin mota ba?” Inji Kwandasta. “Haka kawai, ba za mu biya ba, ai dama an gaya mani irin shegantakarku a nan Legas, shi ya sa na zo da kaina domin in yi maganinku.” Kwandasta ya matsa kaimi cewa dole a biya, don haka abu kamar wasa sai ya koma fada. Bayarabe sai ya dunkula hannuwa da shirin damben zamani na boksin. Shi kuwa Barau ya dunkule hannu daya, ya yi kwanciyar ’yan damben gargajiya. Yana tasowa sai Bayarbe ya yi masa naushi biyu kai tsaye a iduwansa biyu. Nan take Barau ya ce wa dan uwansa: “Audu, haska mani in dauki zaren dambena.” Audu ya ce: “Ai rana ta Barau.” Ya ce cikin mamaki: “Audu, ka ce rana ta?” Audu ya ce: “Awooo, rana ta!” Barau ya ce: “Subhanallahi! To, kama mini guda cikinsu in rama naushina.” Audu ya ce: “Ai mutum guda ne ya yi maka wanga ta’adi.” Barau ya ce: “Koni walla, dama ka fada mini cewa mutanen nan fa shegu na amma nakki na jiya, to yi mini jagora mu isa masauki, domin ba ni gani. Na yarda Yarabawan Legas shegu na ko a kasar Makka!”

Daga Jarma Majid