✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kitimirmirar da ta dabaibaye batun dawo da Rahama Sadau Kannywood

Kitimirmira ta dabaibaye batun dawo da fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau cikin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, tun bayan da ta shiga gidan rediyon…

Kitimirmira ta dabaibaye batun dawo da fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Rahama Sadau cikin masana’antar fina-finan Hausa ta Kannywood, tun bayan da ta shiga gidan rediyon Rahama da ke Kano a ranar Talatar makon jiya bayan ta roki yafiyar Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi na II bisa ga laifin da ta yi na fitowa a cikin faifan wakar bidiyon mawaki Classik mai suna ‘I Lobe U’.

Jarumar ta bayyana neman afuwar ne cikin wani shiri mai suna ‘Ku Karkade Kunnuwanku’, inda ta sha alwashin hakan ba zai sake faruwa ba. 

Idan ba a manta ba dai a ranar 3 ga watan Oktoba, 2016 kungiyar MOPPAN ta bayyana cewa ta dakatar da jarumar daga fitowa a fina-finan Hausa, saboda samunta da laifin yin rungume-rungume da mawakin ne.

Tun bayan korar, abubuwa da dama sun faru, inda jim kadan bayan dakatarwa ta tafi Amurka bayan wata gayyata da fitaccen mawaki Akon da furodusa Zack Amata suka yi mata, inda kuma cikin wata hira da jarumar ta yi da wata jaridar kudancin kasar nan ta bayyana cewa dakatar da ita da aka yi ta bude mata kofofin nasara da kuma ci gaba.

Majiyoyin da dama sun bayyana cewa fitaccen jarumi Ali Nuhu wanda shi ne ubangidan jarumar yake ta uwa da makarbiya wajen ganin an dawo da ita, inda a ranar Talatar makon jiya kuma ya jagorance ta zuwa ofishin Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, inda bayan ganawar ne, suka dauki hoto da shugaban hukumar Isma’ila Na’Abba Afakallah.

Wannan hoto da suka dauka ta sanya aka fara rade-radin cewa Afakallah ya sanya kungiyar MOPPAN ta dawo da jarumar, jita-jitar da ya karyata, ya kuma ce ba ta da tushe ballantana makama.

Ya ce, “Abin da yake faruwa shi ne, Rahama Sadau da Ali Nuhu da kuma daraktanta Yaseen Auwal sun zo ofis dina, sun zo a kan cewa abubwan da take yi ta yi nadama, kuma wadannan abubuwan za su zama na farko da kuma na karshe, don haka tana neman afuwa.”

“Idan ba ka manta ba dama ita kungiyar MOPPAN ita ta tsayar da Rahama Sadau, kuma yanzu ta rubuta takarda ga ita kungiyar MOPPAN din, kuma muna da alaka da kungiyoyin ’yan fim, kuma duk abin da kungiya ta yi to muna goyon bayan abin da zai zama taimako ga ita industuri.” Inji shi.

Ya ce, Rahama ta rubuta takarda ga kungiyar MOPPAN, kuma har yanzu ita kungiyar ba ta rubuto musu takardar cewa sun janye wannan dakatarwar ba.

 “Don haka muna sauraren kungiyar, wurin da ya kama mu shigo za mu shigo, don mu samar da wani yanayi wanda zai sanya kowa ya samu martabarsa ba tare da an danne wani ba, har yanzu ba mu ce komai dangane da batun janye dakatarwar ba, amma Rahama ta ba mu kwafin takardar da ta yi wa ita kungiyar MOPPAN din,”

A nata bangaren kungiyar MOPPAN ta bakin Sakatarenta na Jihar Kano, Salisu Mohammed Ofisa, ya bayyana cewa har yanzu ba su janye batun korar jarumar ba, kuma babu wanda ya ba su umarnin dawo da ita.

Ya ce, “To, abin da ya faru a gurguje shi ne, Rahama Sadau ta shigo Kano, ta samu Ali Nuhu kamar suna da wata matsala tsakaninsu, sun sasanta kansu, kuma daga nan ta yanke shawarar za ta nemi afuwar shugannin masana’antar fim, inda Ali Nuhu ya kai ta Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano, wurin Afakallahu, sannan ta kawo mana wasika a nan MOPPAN, inda ta ba shugaban kungiyar, Kabiru Maikaba, tana neman a yi mata afuwa, a dawo da ita masana’antar fim ta ci gaba da aikinta.

Ya ce har zuwa yanzu babu wani hukuncin da kungiyarsu ta dauka tun lokacin da ta kai musu wasikar, “Mu a kungiyar MOPPAN ba mu zauna mun daddale don mu kalli takardarta ba, saboda ba MOPPAN ita kadai ta kore ta ba, akwai wadansu kungiyoyin ’yan fim da suke karkashinta, sai an kira shugabancin kowace kungiya, kamar yadda aka zauna da su kafin aka sallame ta.” 

Ya ce, a yayin zaman za su duba bayaninta, tun lokacin da aka kore ta yau shekara guda ke nan, “me ya biyo baya? Wadanne irin kalamai ta yi? Ta ci gaba da aikata ire-ire laifukan da suka sa aka kore ta? Shin akwai nadama a tattare da ta? Sai mun tattauna wadannan batutuwa kafin mu ga irin shawarar da za a dauka, don a yafe mata a dawo da ita, ko kuma a dage mata wannan korar ta zama ta wucin gadi zuwa wani lokaci, ko a ci tararta, ko ma a ki yarda ta dawo.”

Ya bayyana dalilin da ya sa ba su yi zaman ba shi ne, shugaban da zai jagoranci zaman, wato Kabiru Maikaba ba shi da lafiya, an yi masa aiki a idonsa, “kuma babu shakka halartarsa zaman yana da matukar muhimmanci, shi ya sa muka ga bai ma dace a yi zaman ba ya nan ba, idan ya samu sauki, to mako na gaba mu yi zaman.”

Ganin ana ta rade-radin cewa Ali Nuhu ne yake uwa da makarbiya wajen dawo da jarumar sai Mujallar Fim ta yi hira da shi, inda ya bayyana cewa sun ziyarci Afakallah ne saboda yana daya daga cikin shugabannin masana’antar.

“E, to, ba wani abu ba ne illa yana (Afakallah) daya daga cikin shugabannin masana’antar fim. Ni dai abin da na tsara yana daga cikin wadanda ya kamata a ziyarta, saboda yaro idan ya yi ba daidai ba aka hukunta shi, kuma har ya gane illar abin da ya yi ba daidai ba ne, ya nemi tuba ko yafiya, to wajen manya za a je a gaya masu….” inji shi.

Ya bayyana cewa jarumar dai ta hanyarsa ta shigo kuma ta yi laifi. “Ni ba zan ce don ta yi laifi kada a hukunta ta ba, dole in goyi bayan a hukunta ta, saboda kowa ya san cewa muna da doka da tsari. Kuma an hukunta ta, kuma abin ya kai kusan shekara guda, tun da kuma tana cikin wani yanayi wanda za ta iya tuba ina ganin ba komai ba ne don an nemi maslaha. Ta kuma nemi in yi mata jagoranci a matsayi na na uba, shi ya sa na yi.”

Ali Nuhu ya bayyana tun da dadewa Rahama take son wannan sasanci. “Wato akwai abubuwa da mutane ba su gane ba game da ’yan wasan da suka yi fice a duniya: yawanci idan irin wannan abin ya faru sukan ja gefe; jan gefen da suke yi kuma ba don ba su isa tunkara ba ne, amma suna ganin cewa idan ma sun yi magana a lokacin kamar ba za a saurare su ba ne. Kamar kai ne danka ya yi maka laifi, ai ba ya shigowa cikin gida, za ka ga ya tsaya a waje yana tsoron idan ya shigo babanshi zai dake shi.”

Mujallar ta tambayi Ali Nuhu ba wannan ne lokaci na farko da jarumar ke aikata laifi ba, sai ya ce, “Ni dai a yadda na kalli Rahama a yanzu, ba na jin za ta kara aikata laifuffuka kamar wadanda ta aikata a baya. Kullum dan Adam girma yake yi yana kara hankali.”