✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kishi ko hauka?

Shi kishi wani yanayi ne na so  da kauna da burin kare abun da ake son daga kamuwa da cuta. Ana kishin kasa kuma ana…

Shi kishi wani yanayi ne na so  da kauna da burin kare abun da ake son daga kamuwa da cuta. Ana kishin kasa kuma ana kishin sana’a da abokan zama.. Duk inda akwai kishi mutane na ganin cewa akwai so, har ma wasu kan ce “kishi so ne”. Duk dan Adam bai cika mutum ba sai ya kasance yana da kishi. Ko dai ya kasance yana kishin kansa, kishin iyalinsa da dai makamantansu. 

Hausawa na cewa “kishi kumallon mata.” Amma a zahiri ba mata kadai ke da kishi ba, har mazan ma suna da shi. Mutane da dama na ganin cewa maza sun fi mata kishi, kawai dai matan sun fi nunawa ne. Wannan abu ne da za a iya muhawara a kai. In har hakan ne, akwai abubuwa da dama da ke silar hakan. A addinin musulunci da kuma al’adar mutanen Afirka da yankuna da dama, maza ne suke auren mace fiye da daya. Su kuma mata miji daya kadai suke aure. Wannan shi ke sa mata su yi ta jin tsoron kawo musu abokiyar zama wadda ake kira kishiya. Kalmar kishiya kanta bai dace ana fadar ta ba, kasancewa zama aka zo yi tare da miji daya ba wai wasa ba. Ita kalmar ke kara wa mata da dama tsoro cikin zukatansu da zarar an furta ta. Sannan kuma maza da dama sukan fara wulakanta uwargida idan amarya ta zo. Ita da ‘ya ‘yanta su zama ko oho. Su ma amaren su yi ta jin dadi cewa ana wulakanta uwargida, ba sa tunanin cewa su ma idan aka yi sabuwa, haka za a yi masu. Hakan na matukar tsoratar da mafi yawancin mata, har ma ka ji suna cewa “ba kishiyar ake tsoro ba sai sharrin ta”.

Yarda da amincewa na da matukar muhimmanci a dukkan tarayya, musamman ma ta aure. Da zarar babu yarda a cikin zaman aure, zargi zai shigo ciki kuma ba za a taba samun zaman lafiya ba. Ya kamata mu rika gina aure bisa yarda da amincewar juna, don hakika su ne gishirin zaman aure. Rashin yarda ne ke kawo rashin jituwa har ta kai ga rikici, a wasu lokutan ma har da kisa.

Shin kishi hauka ne? 

 Shin wadanne irin halaye ne idan mutum yana yi za a kira su kishi?  Kuma wadanne halaye ne za a ce hauka? Kawai bambanci tsakanin kishi da hauka. “Kishi ba hauka ba ne” inji malam bahaushe. Shi kishi akwai shi a musulunci, don Manzon Allah (SAW) ya ce Allah na fushi da wanda ba ya kishin iyalinsa.

Kwanaki muka ji labarin yadda wata budurwa a Legas ta soka wa saurayinta almakashi don ta kama shi yana hira da wata. Take ya rasa ransa. Akwai misalai da yawa da ke faruwa a wannan zamanin. A makon da ya gabata ma muka samu mummunan labari cewa ana zargin wata mata da soka wa mijinta wuka a wurare daban daban, don ta ga yana magana ta sakon waya da wata. A Ingila ma an samu mijin da ya kashe matarsa don ta ce masa za ta rabu da shi ta auri wani da take so. Wai shin wannan kishi za mu kira shi ko hauka? Ta yaya za ka ce wai wanda kake ikirarin kana kauna kuma ka kashe shi? Kun ga an samu matsala ke nan. Kamar yadda muka fada a baya,  kishi shi ne kare mutum daga dukkan cuta. To ta yaya za ka kashe mutumin da kake so  kuma ka kira shi kishi?

Akwai gwaje- gwaje da dama da ake yi kafin aure wadanda aka maida su dole, kamar cutar kanjamau (HIb/AIDS), genotype, hepatitis, blood group da sauransu. To mai zai hana a rika gwajin kwakwalwa? Mutane da dama bayan aure suna zautuwa, amma da an yi wannan gwajin da an nemi magani ko dai wata mafita. Ciwon hauka fa ba sai mutum yana yawo a titi yana cin datti ba. Sai ka ga mutum kamar lafiyarsa lau a zahiri, amma kwakwalwarsa ba kalau take ba.

A farko dai mun ce kishi so ne, a nan kuma mun fadi cewa kishi ba hauka ba ne. Ko a kira irin wadannan halaye rashin tarbiya, ko tabarbarewar zamani, ko a kira shi hauka, wannan ya rage na mai karatu. 

Abubuwa da dama na faruwa ne saboda tabarbarewar tarbiyya na wannan zamanin. Iyayen zamani sun yi tarbiyyar yaran zamani. An kawo matakin da dole ne mu yi nazari, mu yi gyara. Kuma yin gyara ba wai kawai akan rubuce rubuce cewa tarbiyya ta lalace ba. Mu fara da kanmu. Mu yi wa kanmu karatun ta natsu sannan mu yi  wa ‘ya ‘yanmu da kannenmu tarbiya mai kyau. Kuma mu tuna a kodayaushe cewa idan icce yana danye ne ake iya tankwara shi, idan ya bushe kuwa, sai dai ya karye. Haka kadai idan ka yi ya fi a kan duk wasu maganganu da za ka fito ka yi. Ban ce kar a fadakar ba, amma ya kasance ana amfani da irin abubuwan da ake fadakarwar a aikace, ba a baki kawai ba.

Shi dai kishi son juna ne, ba wai kashe juna ba kuma ba hauka ba. Ya kamata mata a rika kishi yadda ya dace, su kuma maza a rike gaskiya da amana. Domin soyayya da kishi mai kyau yana faruwa ne idan har an gina son a kan gaskiya da amana. Ba a kan karya da cin mutunci ba.

Sau da yawa ana samun inda mata ke nema wa mazansu wadda za su aura saboda zaman lafiya da mutunci. Amma kuma sau da yawa wadansu sukan manta da cewa uwargidar ce ta ba da shawara har aka auro su, ta yadda da sun zauna, sai kishi ko hauka ya sa su ga ba su da makiyi sai uwargidar. 

Don haka mu nemi zaman lafiya, mu rage kishin banza (na hauka), mu rike kishi na gaskiya ta hanyar kula da maza da matanmu yadda ya kamata. Ta haka ne za mu zauna lafiya. Hausawa dai suna cewa “idan kunne ya ji, gangar jiki ta tsira”

 

Daga Zainab Mukhtar. 07081693830