Masauratar Bichi ta ware ranar Juma’a domin gudanar da sallah da addu’o’i na musamman domin neman samuwar zaman lafiya a fadin Najeriya.
Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, ne ya ayyana ranar a sakon ta’aziyyarsa gami da bayyana takaicinsa kan kisan gillar da ’yan bindiga suka yi wa matafiya a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato a makon jiya.
- Monguno ya bayyana sunayen kungiyoyin da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya
- Buhari ya roki Ganduje filin gina tashar wutar lantarki a Bichi
Sanarwar da Masarautar Bichi ta fitar ta hannun Sakatarenta, Alhaji Abubakar Ibrahim Yakasai, ta ce, “Mai Martaba Sarki na umartar daukacin al’ummar Bichi da su fito domin halartar addu’o’i na musamman a safiyar ranar Juma’a, 17/12/2021 a Babban Masallacin Bichi domin yin salloli tare da mika wa Allah bukatunmu;
“Za mu gudanar da addu’o’i na musamman, mu roki Allah Ya kawo mana dauki a wannan yanayi da muka tsinci kanmu a ciki, Ya kawo wa al’ummarmu zaman lafiya da za su samu damar ci gaba da gudanar da harkokinsu ne neman halaliya.”
Sanarwar ta kuma mika gaisuwar ta’aziyyar masarautar da daukacin al’ummar Bichi ga Gwamnatin Jihar Sakkwato da Fadar Sarkin Musulmi da al’ummar Jihar Sakkwato da ta Musulmi kan kisan gillar da aka yi wa matafiyan.